Azumin Ashura ko dai Koyi Da Yahudawa ??


* MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES

Duk wani aiki na ibada ana samun ladansa be idan ya kasance yayi daidai da koyarwar addini ta hanyar Manzo (S.A.W.W), ko kuma bayin Allah salihai. Sannan akan sami ladansa ko da mutum ne ta qirqiro shi matuqar bai sabawa koyarwar Manzo (S) ba.

Amma shi azumin Ashura ya sabawa koyarwar addini, qirqiro shi akayi don bishe ta'addancin gidan Banu Umayyah (L A). A dalilin haka suka qirqiro hadisai masu cin karo da juna kamar haka:-
(1)- Bukharin ya riwaito cewa, Baban Ma'ammar ya bamu labari, Abdul Warith ya bamu labari, Ayuba ya bamu labari , Abdullahi Bn Sa'id Bn Jubair ya bamu labari daga babansa, daga Ibn Abbas (R A) yace;
" Annabi (S.A W W) ya isa Madinah sai yaga Yahudawa na azuntar ranar Ashura, sai yace; " MENENE WANNAN ?"
Su kace, ai wannan rana CE saliha. Ita ce ranar da Allah ya tseratar da Banu Isra'ila daga maqiyansu, Musa ya azumceta. Yace;
" AI MU MUKA FI CANCANTA DA MUSA FIYE DA KU ."
(Bukhari:2004)
(2)- Abdullahi Bn Mas'ud ya bam u labari daga Malik, daga Hishan Bn Urwata, daga babansa, daga A"isha (R.A) tace;
" QURAISHAWA SUN KASANCE SUNA AZUMTAR RANAR ASHURA A JAHILIYYA, KUMA MANZO (S) YA KASANCE YANA AZUMTARSA. YAYIN DA AKA FARARTA RAMADANA SAI YA BAR (azumtar) RANAR ASHURA, WANDA YASO YA AZUMCETA, WANDA YASO YA BARTA ."
(Bukhari:2002).

A hadisin farko an nuna cewa Annabi (S) bai san da wannan azumi ba, ana biyu kuma akace dama can yana azumtarsa.
To, shin wannene gaskiya a cikinsu?
Daga wakilanmu na Bauchi Zone.

Tare da Ado Isah Guda.
(08137925934-08126385470)

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post