ZAMAN MAKOKIN IMAM HUSSAINI A DA'IRAR KADUNA-MA'ASUMA NIGERIAN NEWS UPDATE
A yau alhamis 01/01/1442 'yan uwa musulmi mabiya Sheikh Ibrahim Zakzakiy dake cikin garin Kaduna suka fara shirya zaman makoki domin tunawa da kisan gillar da aka yiwa jikan Manzon Allah Sayyadina Hussaini a filin Karbala.
Wakilin almajiran Sheikh Zakzakiy na Da'irar Kaduna da kewaye wato Sheikh Aliyu Tirmidhiy ne ya jagoranci zaman, inda kuma Malam Aminu Abubakar badiko ya zama babban bako a gurin,Babban bako mai jawabi Malam Aminu yayi jawabai masu tsayin gaske, kuma ya baiwa maudu'in da aka bashi hakkinshi na muhimmancin zaman makokin Imam Hussaini da kuma yadda ya kamata masu zaman makokin su kasamce.
Tun a farko dai malamin ya fara fado muhimmancin yin zaman makokin da kuma ladubban zaman makokin kamar irin mutum ya kasamci cikin yanayi na bakin ciki tun ranar daya ga wata har bayan goma ga wata alal aqalla, da kuma yin ziyarorin Imam Hussaini da yawaita sallama a gareshi.karshe malamin ya ambato falalar yawaita yin kuka a tsakanin kwanakin goma.
Daga karshe malam Aliyu Tirmidhiy yayi gajeren bayani ga 'yan uwa a takaice, sannan akayi wakokin juyayi akai addu'a aka sallami kowa.
-Jabeer Bin Said Al'ansariy.
-01/01/1442.
-20/08/2020.
-MNU 016.