.
.
Wannan tambaya ce wacce amsarta ba za ta Samu da kundin ka ba, sai anyi nazari sosai don batun ilimi ne.
To, saboda haka za mu leqa manya daga cikin littafan hadisai ba Ahlus-Sunnati don sauqaqa amma wannan tambaya.
.
(1)- Bukhari ya riwaito cewa; Aliyu ya ba ni labari, Sufyanu ya ba mu labari, Amru yace; daga Hassan Bn Muhammad, daga Jabir Bn Abdullah da Salamata Bn Ak'wa'a suka ce; mun kasance cikin runduna sai 'Dan Aiken Ma'aikin Allah ( S.A.W.W ) yazo mana yace;
" LALLE ANYI MUKU IZININ YIN MUTU'AH, KUYI MUTU'AH !"
.
- Bukhari, hadisi mai lamba 5118.
- Muslim, J:13, Sh:1405.
.
========== DARASI ==========
________________________________________
Darasin da ke cikin wannan hadisi shine, it Mutu'ah ba a soma yinta ba sai da umarni yazo daga Allah da Manzonsa ( S.A.W.W ). Kuma da can kafin umarnin ba a san sunanta ba ma ( MUTU'AR ) ballantana yarda ake yinta.
.
(2)- Bukhari ya sake ruwaitowa daga Musaddadu yace; Yahya ya ba mu labari daga Imrana baban Bakin; baban Raja'i ya ba mu labari daga Imrana Bn Hussain (R.A) yace;
" AN SAUKAR DA AYAR MUTU'AH CIKIN LITTAFIN ALLAH, KUMA MUN AIKATA TA TARE DA ANNABI (S.A.W.W), QUR'ANI BAI SAUKO DA HARAMCINTA BA, KUMA ( Annabi ) BAI YI HANI A KANTA BA HAR YA MUTU, WANI MUTUM NE KAWAI YA FADI ABINDA YASO ( na haninsa gare ta ) DA RA'AYINSA ."
.
( Bukhari, hadisi mai lamba 4518 ).
.
========== DARASI ==========
__________________________________________
Wannan hadisi ya fitar mana da darusa kamar haka:-
.
(i)- Babu wani haramci daga Allah a kanta.
.
(ii)- Haka ma daga Annabi ( S.A.W.W ) ba a sami hani ba.
.
(iii)- An sami wani Wanda shi ba Allah bane, kuna ba Manzonsa ba, amma ya hana bisa wani ra'ayi nasa Wanda shi yasan dalilin hakan.
.
(3)- Bukhari ya sake riwaito wani hadisi cewa; Maluku Bn Isma'il ya ba mu labari; Ibn Uyainata ya ba mu labari cewa ta Ji Zuhriyyu yana cewa; Hassan Bn Muhammad Bn Aliyu da dan'uwansa Abdullahi Bn Muhammad sun ba ni labari daga babansu; Cewa Aliyu (R.A) ya fadawa Ibn Abbas (R.A) cewa;
" LALLE ANNABI (S.A W.W) YAYI HANI GAME DA MUTU'AH, DA KUMA NAMAN DABBOBIN DA AKA HALASTA CIN SU RANAR KHAIBARA ."
.
( Bukhari, hadisi mai lamba 5115 ).
.
========== DARASI ==========
__________________________________________
Wannan hadisi kuwa nuna mana take, shi auren Mutu'ah Annabi (S.A.W.W) yayi gani à Kansas kafin yabar duniya.
.
.
========== NAZARI ==========
________________________________________
.
Idan muka nazarci hadisi na biyu dana uku za muga cewa suna cin karo da juna.
Domin na biyu yana tabbatar da hadisin farko ne tare da Kore dukkan wata magana da za ta ce an haramta auren Mutu'ah. Yayin da hadisi na uku ke Kore halascin Mutu'ah a muslimci baya wafatin Ma'aiki ( S.A.W.W ).
.
=========== TAMBAYA ========
________________________________________
.
DAN ALLAH CIKIN HADISANNAN WANNENE GASKIYA?
.
ME YASA YA ZAMA GASKIYA 'DAYAN KUMA YA ZAMA QARYA?
.
TO, YANZU MENENE MATSAYIN AUREN MUTU'AH BISA NAZARIYYAR WADAMNAN HADISAI?
.
DON MEYE AKA SAMI CIN KARO CIKIN SAHIHAN LITTAFAI?
.
IDAN ANA SAMUN IRIN WANNAN CIN KARON, LITTAFAN SUN CANCANTA A KIRA SU INGANTATTU?
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com