ANYI MASA BULALI:- Sakamakon Zuwa da karamin yaro masallachi...

Wani hakimi a Jihar Katsina ya sa an lakadawa wani tshohon soja mai kimanin shekaru 80 duka, aka Kuma tsare shi tsawon kwana 3, a dalilin Yana zuwa da karamin yaro masallaci.


wannan abun takaici ya faru ne, a garin Rimi dake jahar Katsina, bayan da wasu mutane Suka nemi cewa, wannan tsohon soja Mai suna (Yusuf Soja) ya daina zuwa da karamin yaro a masallaci, saboda yana yi masu rashin ji, shi Kuma ya ce ba zai daina zuwa da shi ba, saboda ko a lokacin Manzon Allah (saw) Ana zuwa da yara masallaci.

A dalilin haka, sai suka Kai kararsa ga hakimin Rimi, Wanda a nan ma ya tabbatar wa da hakimin cewa ba zai daina zuwa da yaro masallaci ba, tunda shari'ar musulunci ba ta hana ba, hasali ma, umarni ta yi da a koya wa Yara kanana Sallah. Don haka sai hakimin ya ce ya raina shi, ya sa dogarawa suka yi ta dukan sa da bulali, sannan aka tsare shi a fadar hakimin tun safiyar asabar 08/08/2020, har zuwa marecen ranar litinin 10/08/2020 aka sake shi ya koma ga iyalansa.

Kafin cin zarafin wannan tsohon soja, matarsa aka fara cin zarafinta, Mai suna (Karima Yusuf) Mai kimanin shekaru sittin da haihuwa, inda hakimin ya sa aka lakada mata duka, a sakamakon ta ki amincewa wani makwabcin filinta yayi gini akan santa/titi.

A dalilin wannan cin zarafi ne, ta Kai koke ga Hukumar Kare hakkin dan Adam ta kasa reshen jahar Katsina, wato (National Human Right commission) Wanda tsawon wata bakwai ko takwas da Kai wannan koke, amma har yanzu babu wani takamaiman mataki da Hukumar ta dauka na bi mata hakkinta.

To daman wannan ba bakon abu ba ne a Najeriya idan ka ga hukumomi na azarbabi a kan lamari, za ka samu talakka ne Wanda ba ya da galihu ya aikata wani abu yanzu ace wannan dattijo da ya sadaukar da rayuwarsa, yayi yaki don samun zaman lafiyar Najeriya, Wanda har yanzu akwai karfe a jikinsa, a dalilin harbin bindiga (a lokacin yakin Biyafara), ai bai cancanci a wulakanta shi ba, "inji wasu da ke tofa albarkacin bakinsu kan lamarin"

Zuwa yanzu dai ba wani abina oka tayi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post