ANNABI ADAMU ( AS ) A FILIN KARBALA .


 An Rawaito cewa ; Lokacin da Allah Ta'ala ya saukar da Annabi Adamu ( AS ) kasa , bai ga Hauwa'u a tare da shi ba , sai ya shiga Duniya yana nemanta  ya je nan ya je can wata rana a cikin tafiyarsa sai ya bita Karbala, yana zuwa Saharar sai yaji wani bakin ciki ya kama shi kirjinsa ya yi kunci , yana zuwa daidai inda za a kashe Imam Hussain ( AS ) sai ya yi tuntube , Jini ya rinka fita a kafarsa.

 Sai ya daga kai sama ya ce ; “ Ya Ubangiji ! Shin na aikata wani laifi ne kuma aka azabta ni da shi ? Domin na yi yawo ko ina a bayan kasa ba abin da ya same ni , sai a wannan rerayin ! ” .

 Sai Allah ya yi masa Wahayi cewa ; Ya Adamu  Ba ka aikata wani Zunubi ba , sai dai a Wannan Rerayin ne za a kashe Danka Hussaini bisa Zalinci , shi ne jininka ya zuba a wurin don ya hadu da jininsa ,. " Sai Annabi Adam ( AS ) ya tambaya ; “ Shin Hussainin Annabi ne ? Sai aka ce masa ; “ Ala , shi Jikan Annabi Muhammad ( S ) ne ” , Sai ya tambaya ; “ Waye zai kashe shi ?

" Sai aka ce masa ; Wanda zai kashe shi shi ne Yazidu Tsinanne a Sama da kasa ! " Sai Adamu ( AS ) ya ce ; “ Ya Jibrilu ! Me zan yi ( wa makashin Hussaini ? ) " Sai ya ce ; ka tsine masa ! " , Sai Annabi Adamu ( AS ) ya tsinewa Yazidu har sau 4 , sannan ya wuce Dutsen Arfa ya samu Nana Hauwa'u a cen ' [ Bihar , 44 242 ].

🌹Ibn Musa Baba Potiskum 🌹

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah ya tsinewa Yazidu,Allah ya tsinewa Yazidu,Allah ya tsinewa Yazidu!!

    ReplyDelete
Previous Post Next Post