Amurka Ta Sake Shan Kaye A Kwamitin Tsaro Na MDD Dangane Da Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawavad Zarif ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka a karo na biyu ta sake zama saniyar ware a kwamitin tsaro na MDD.

Zarif ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter bayan da shugaban kwamitin tsaro na MDD na yanzu ya mayarwa Mike Pompeo jawabin bukatarsa na maida takunkuman tattalin arziki wanda kwamitin na dorawa kasar Iran don ta sabawa kudurin majalisar dinkin duniya ta 2231.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa mafi yawan mambobin kwamitin basu amince da bukatar ta Amurka ba, don haka y ace ba abinda kwamitin zata sake yi kan wannan batun.

A ranar Alhamis 20 ga watan Augustan da muke ciki ne sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pomoeo ya mikawa kwamitin tsaro wannan bukatar, sannan a ranar Jumma’a 4 daga cikin mambobi masu kujerun din din din da kuma wasu mambobi 9 suka bayyana cewa bukatar Amurka ba ta bisa kan ka’ida.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post