​Al’ummar Falastinu Na Ci Gaba Da Yin Tir Da Matakin Gwamnatin UAE Kan Kulla Hulda Da Isra’ila

Al’ummar Falastinu suna ci gaba da mayar da martani a cikin fushi a kan gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, dangane da bude huldar Diflomasiyya da ta yi tare da gwamnatin yahudawan Isra’ila.


Rahotanni daga Falastinu na cewa, Falastinawa suna ci gaba da gudanar da jerin gwano a birane daban-daban suna rera taken cewa mahukuntan UAE ma’inta ne.


Masu zanga-zanga sun taru a gaban masallacin Quds mai alfarma, suna daga hotunan yariman UAE mai jiran gado Muhammad Bin Zayed, suna kiransa da maha’inci, tare da soke hotunansa da jan fenti.


A nata bangaren gwamnatin Falastinu ta janye jakadanta daga birnin Abu Dhabi, tare da jaddada cewa ba zai sake komawa ba, matukar dai UAE tana da huldar diflomasiyya da gwamnatin yahudawan Isra’ila.


A nasu bangaren kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa da suka hada da Hamas da kuma Jihadul Islami da sauransu, sun fitar da bayanai daban-daban da ke yin tir da Alladawai da wannan matsaya da UAE ta dauka, tare da bayyana hakan a matsayin babban abin bakin ciki, ta yadda sarakunan larabawa suke karkata ga yahudawa suna hada kai da su, tare da yin watsi da al’ummar Falastinu.


A kasashen duniya daban-daban, kungiyoyin musulmi da na larabawa na ci gaba da mayar da martani mai zafi kan wannan mataki na UAE, tare da nuna goyon baya ga al’ummar falastinu.


SOURCE: ABNA24.COM


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com 


ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post