" YAA ALLAH, KA JI QAN MAGADANA (har sau uku) ." Aka ce; Yaa Manzon Allah su waye ne magadanka? Yace;
" WADANDA ZA SU ZO A BAYANA, SUNA RUWAITO HADISAINA DA SUNNAH TA, KUMA SUNA KOYAR DASU GA MUTANE ."
*
(Kitabul-Wafi, SH;146).
*
== ABIN LA'AKARI ==
*
Su wadannan masu riwaito Hadisai da Sunnoni ba wai ana nufin duk wanda ya bude baki ko ya sanya alqalami wajen kawo son zuciyarsa ko wanke wani mai jiki da kashi bane.
*
A'a, ana nufin masu riwaito haqiqanin abinda ya gangaro daga gare shi ne (S.A.W.W), domin maqaryata masu kwaso maganganun qarya don cimma muradinsu.
*
Wannan dalili yasa Annabi (S.A.W.W) yace;
" DUK WANDA YAYI MIN QARYA DA GANGAN (don ciyan buqatar kansa), TO YA NEMI GURIN ZAMANSA A WUTA ."
*
To, ba irin wadannan miyagun ake nufi ba.
*
'DAN'UWA, NEMI MASU KOYAR DA HADISAN ANNABI NA GASKIYA DON KADA KA HALAKA!