- Jawabin Shiekh Zakzaky (H)
A wannan lokaci kuma sai aka zo mana da wasu fitinoni iri-iri na rarraba, na cewa mu 'yan kaza ne da 'yan kaza ne. Zaka ga mutum da hancin sa yayi baki saboda zukar sholusan, ni ba wai na raina masa bane kan zukar shuloshon, amma akwai laifin al'umma, don ita ta jefa shi akan shan sholushon din.
Don da yana samun aikin yi yana samun rayuwa lafiya lau ba yanda za'ayi yace shi bazai yiba sholusho zai sha. Tilas ta sa shi shan sholishon ko ba komai ya dan huta. Tunda in ya manta da matsalarsa shi kenan. Naji ma ana hira da wani dan sholusho yace wahala ce da yunwa.
Yunwa ta damesu bassuda aikin yi. Yace to shi kenan in ya sami dan sholushosa yadan zuka ya je ya dan sami wani kongo ya labe, sai ya ganshi a gida mai 'Air Condition' ya shiga wata zungureriyar mota kuma. Yace to su nasu jin dadin kenan. Saboda an haram ta musu jin dadi.
Kuma ko yan farautar nan da kake gani, ko yan tauri ba wanda yake so yayi wannan, tilas ta sa shi. Ko dan wiwi inda da abun kirki ba zai ce shi ba zaiyi wannan ba, za shi yaje yayi farauta ne ya kama gafiya. Takai ma duk gafiyoyin gari an kame su. Suka shiga cin kyanwa. Harma ana ce mata zomo mai dogon bindi. Duk sun kwashe kyanwan gari.
Don ta kai ma 'yan uwa akwai wani lokaci da aka kai su kurkuku suka zauna tare da dan limamin wani gari. Shi dan limamin din an kawo shine shi ma kurkukun saboda ana tuhumar sa da ya sace kare. Saboda yakan mangare kare ma a cinye.
Dubi yanda aka talauta mutane aka maishe su ga su nan kawai kamar wasu dabbobi. Mutane da ya kamata ya zamana sune taurari da suke haskaka al'Umma. Wanda su ya kamata ace su jagoranci al'umma, an maishe su ga su jahilai matalauta. Kuma koma kayi karatun to sai an maishe ka zauna gari banza. A lokaci guda aka kawo fitinar kai dan kaza ne, kai dan kaza ne. Me ya kawo wannan?.
Bamu samu daukaka a sana diyyan mu yan bangare kaza ne ba, ko mu yan kaza ne ba. Allah ya daukake mune da darajan wannan addini. Kuma mu kara koma wa ga addinin nan shine abinda yake mafita gare mu.
Wannan wani bangare ne a cikin littafin DARASIN ASHURA na Sayyid Zakzaky wanda cibiyar wallafa da yada ayyukan Sheikh Zakzaky (H) suka buga.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com