Me ake tsammani daga garken dabbobin da suka rasa makiyayi? Shin abincin da za su ci ne ya fi muhimmanci a gare su a lokacin ko kuwa samuwar makiyayin?
Bisa tozon wannan sikeli ne nake ganin wallen mai cewa wai al'amarin halifancin Annabi (sawa) ya riga ya wuce, a bar batun kawai. Ya kasa gane cewa sharadin daidaituwar lamurran Musulunci ya ta'allaqa ne da wilayar Ahlulbaiti (as) saboda mashahuriyar ruwayar da ta ce a yi riqo da su da Qur'ani.
Mene ne zai sa Annabi (sawa) ya ce "Na bar mu ku Qur'ani da Ahlulbaiti, in har kuka yi riqo da su, ba za ku bace a bayana ba har abada?" Wace hikima za ta sa Annabi (sawa) ya yi ta nanata cewa, "ina tunatar da ku Allah game da haqqin Ahlulbaitina" kamar yadda Muslim ya ruwaito a sahihinsa? Wace gafalalliyar al'umma ce jagoranta zai ce ta bi wannan hanyar amma sai ta fandare kuma ta yi tunanin al'amuranta za su gyaru?
Kalla! Summa Kalla!!
Madamar al'ummar Musulmi ba su yi riqo da Ahlulbaiti (as) ba, to WALLAHI ba za su taba ganin daidai a al'amuransu ba. Misalinsu shi ne misalin garken dabbobin can da ya rasa makiyayi. Don haka suke a tarwatse.
-MBI
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Taskar ilimi