Manzon Rahma (S) a karshen aikensa, (sakon da ya isar daga wajen Ubangijinsa), bayan ya isar da kusan komai na addini don dama haka Allah (T) ya tsara bisa hikimarSa, isar da sakon Manzon Allah ba gaba daya aka yi ba, a hankali- a hankali aka yi, Manzon Allah kuma yana bayani a hankali- a hankali. Yayin da al’amarin (wannan addinin) ya kusa kamala. Sai Allah ya aiko Manzonsa (Jibrilu kenan) izuwa ga Annabi Muhammad (S), yace masa; ‘Ka isar da duk addini, illa yanzu abu biyu suka rage; Ka yi hajji, ka nunawa Muminai yadda za su yi Hajji, sannan akwai kuma wulaya (wato za ka fada musu wanda za su bi a bayanka), domin yanzu bayan isar da sakonka z aka koma i zuwa ga Ubangijinka.’
Saboda haka sai Manzon Allah (S) ya sa aka yi yekuwa, ba kawai a Madina ba, har a dukkanin sassan (garuruwan) da Muminai suke, duk wanda Allah ya horewa halin zuwa Hajji, to ba a dauke masa ba. Saboda haka sai duk Muminai a duk inda suke suka yi aniya, daga duk inda suke suka kama hanyar zuwa hajji a wannan shekarar ta 10 da hijira. A lokacin Manzon Allah (S) ya riga ya tura Imam Ali (AS) zuwa Yaman.
Don haka sai ya aika masa cewa daga Yaman din shima ya wuce zuwa Hajji su hadu a Makkah. Manzon Allah ya shirya ya fita daga Madina, ya tsaya a Zulhulaifa, inda ya nunawa mutanen Madina mikatinsa, kuma ya yi Ihrami, ya koyar da su yadda ake Ihrami. Ya fita ne a ranar Asabar Zulkada ya rage saura kwana hudu ko biyar (wato 25 ko 26 ga Zulkada, a shekara ta 10 bayan hijira), aka ce wadanda suka taho wannan Hajjin tare da shi (daga Madina), adadinsu ya kai mutum 120,000, daga wadanda suka tafi hajji tare da shi har da Siddikatud Dahira, Fatimatuz Zahra ‘Yarsa (SA) da Ummu Hani ‘yar uwan Amirulmuminin (AS), da Nana Ummu Salama da sauran matan Annabi (S) daga cikinsu akwai A’isha da Hafsa. Da sauran mutane daban-daban.
To, bayan nan, Manzon Allah (S) ya isa Makkah, yai Dawafi da Sa’ayi, ya yi saisaye ya cire Ihrami, ya nuna musu an gabatar da Umra yanzu saura hajji kenan. Suka zauna wadansu kwanaki kafin ranar Tarwiyya. A cikin wadannan kwanakin Ali (AS) ya iso daga Yaman. Manzon Allah ya tambaye shi wane irin Hajji ka yi niyya? (Kun san a wajen Ihrami mutum yana cewa ya yi harama da hajji iri kaza. Akwai hajji da ake ce
ma Ifradi wanda yake mutum idan ya yi Ihrami ba zai cire ba har sai ya gama hajjin.
Akwai kuma Tamattu’i, wanda yake mutum yana gabatar da Umra sai ya cire Ihraminsa ya zama kamar mazaunin gari, sannan kuma lokacin hajji ya sake Ihrami ya tafi hajji, ya raba umra daban Hajji daban kenan, alhali shi mai Ifradi shi Hajji kawai yake yi, sai bayan ya gama Hajjin sannan daga baya ya yi Umra. Akwai kuma mai Hajjin da ake ce ma Qirani, wanda shi zai hada Umra da Hajjin ne a lokaci guda. A lokaci guda zai yi niyya biyu, ba sai ya gama wanan sannan ya yi wanna ba). To, Manzon Allah (S) ya yi niyyar Tamattu’I ne, saboda ya gabatar da Umra ya warware.
Da Imam Ali (AS) ya iso, sai yace masa, wane irin hajji ka yi niyya? Sai Imam Ali (AS) yace; ‘Cewa na yi, Ya Rabbi na yi Ihrami da irin Hajjin da Manzon Allah (S) ya yi Ihrami da shi.’ Sai Manzon Allah (S) yace, “Ya yi daidai. Dama Tamattu’i na yi, kana iya warwarewa.” To bayan ya yi Dawafi da sa’ayi sai ya warware. Suka
zauna nan a garin Makkah. To, suna sallah, kuma jama’a na dafifi ga Manzon Allah (S) a wannan lokacin ne abubuwa da dama suka auku.
Daga ciki akwai lokacin da Manzon Allah (S) ya musu bayani, yace musu; Ubangijina ya min bayanin cewa komai na addinin Musulunci an gama saukarwa, in bada abubuwa guda biyu da suka rage, sune; na koya muku Hajji, na kuma nasabta wanda zai gaje ni a bayana. To, ko da ya fadi haka nan, sai ya ga fuskokin wasu sun yi wani iri (sun kwakkwansare fuska) suna tunanin sun san wa ake so a nasabtamusu. Don haka, Allah (T) cikin hikimarsa sai ya fara musu nune da ishara da isharori.
Isharar farko ita ce saukar ayar ‘Innama waliyukumullah….’ Lokacin Manzon Allah (S) yana tare da mutane kuma Ali (AS) yana gefe guda yana salla, sai wani mai bara ya zo ya yi bara. Sai Manzon Allah (S) yace, wa zai bashi sadaka? Sai ba a samu wanda ya bashi sadakan a cikin wadanda suke zazzaune ba. Har manzon Allah ya yi wadansu kalamai wanda ya kamata su kwadaitar da mutane su zabura wajen mika sadakar, amma dai ba a samu wanda ya zabura ya ba mabaracin sadakan ba.
To shi Imam Ali (AS) ya ji wannan alhali yana halin ruku’u a Sallah, sai ya yi ishara ga mai baran, ya mika masa hannunsa ya nuna masa zobensa (ishara ga cewa ya zo ya cire zoben nasa), to sai ya je ya zare zoben. To wannan ya faru ne a ji da ganin mutanen da ke wajen. Sai ga aya ta sauka, Allah (T) yana cewa: “Innama waliyukumullahu wa Rasuluhu wallazina amanul lazina yukimunan salata wa yu’utunaz zakata wa hum raki’un.” (Suratul Ma'ida, aya ta 55). Wato, “Wanda za ku jibintawa al’amarinku (wanda za ku bi), Shine Allah da ManzonSa da Muminan da suke tsayar da sallah suke ba da sadaka a halin suna ruku’u.” Sai Manzon Allah (S) ya yi kabbara.
To, su wane ne muminan da suke ba da sadaka suna cikin ruku’u? Ali (AS) ne. Don haka ko da aya tace, ‘…da muminan da suke ba da sadaka suna ruku’u’ ishara ce ga Imam Ali (AS). Domin Allah (T) yace ne; “Sun aba da zakka a lokacin suna halin ruku’u.” Wannan abu a bayyane Amirulmuminin Ali (As) ne ya yi hakan. ‘Jumla haliyya’, wato yayin da suke ruku’u din ne suke ba da sadakan (zakkar).
To, bayan Manzon Allah (S) ya karanta wannan ayar sai ya ga wasu fuskoki sun kwakkwansare. Wato an yi ishara “Wanda za ku bi Allah ku bi ManzonSa ku bi Ali.” Ayar bata ce Ali (AS) ba, balle suce da Manzon Allah (S) ana masa wahayi yanzu ya zo da wani abu, sai Allah ya siffanta shi da siffar aikinsa. ‘Masu ba da sadaka suna ruku’u.’
To, sai Manzon Allah (S) da ya dubi wannan, sai ya tashi ya je ya tsaya gaban Ka’aba duk suna saurarensa, yace; “Ya Allah, Kai ne dan uwana
Musa ya roke ka yace da kai, ‘Waj’alli waziran min ahali, Haruna Akhi, ishdud bihi azri, wa ashrikhu fi amri, kai nusabbihaka kasira wa nazkuruka kasira, innaka kunta bina basira.’ Sai ka amsa masa da cewa; ‘Kad utita su’ulaka ya Musa.’ To nima ina rokonka kamar yadda dan uwana Musa ya roka. Nima in ace maka; ‘Ya Allah, Ij’alli waziran min ahali, Aliyun Akhi, Ishdud bihi azri, wa ashrukhu fi amri, kai nusabbihaka kasira wa nazkuruka kasira, innaka kunta bina basira.’
Nan take sai aka ji Manzon Allah (S) yace; ‘Allahu Akbar! Yanzu ga Jibrilu nan yace da ni ‘Kad utika su’ulaka Ya Muhammad.’ Sai fuskokin wasu daga wadanda suke tare da Annabi (S) ya kuma baci a karo na uku, saboda haka Manzon Allah (S) ya sa abin da zai iya faruwa, don haka, ranar 8 ga wata aka yi Tarwiyya aka yi Ihrami aka fita, da daddare, ana gobe in gari ya waye za a je Arfa, sai Manzon Allah (S) yace musu; Gobe in Allah ya kaimu mun je Arfa zan ayyana magajina a bayana. Sai ya sake ganin fuskoki sun kara muni kamar duhun dare.
Da ya dube su yaga fuskoki sun kwakkwansare, sai yace to fa! Ina fuskantar bijirewa kamar yadda na fuskanta daga mutanen Kuraishawa a lokacin da na zo musu da ‘La’ilaha illallah Muhammadur Rasullalah.’ Wadanda kuma suka amsa mini a ‘La’ilaha illallah Muhammadur Rasullalah.’ Yanzu kuma sune za su bijire min, irin yadda akai min na farko, amma wannan ya fi wancan hadari. "Don ku sani, wannan abin da za a kaddamar, wanda bai yarda da shi ba kamar bai yarda da ‘La’ilaha illallah Muhammadur Rasullalah’ bane." To, sai ya ga rai ya baci dai.
Kashe gari Manzon Allah (S) ya tafi Arfa ya yi wata huduba mai tsawo, wacce a littafan Ama sukan kawo bangarorinta, amma ba za ka ganta cikakkiya ba a wajensu. Alhamdulillahi, Malamanmu (Na Imamiyya) sun ruwaito Hudubar Manzon Allah (S) na Arfa kammalalliya. Cikin abin da yake cewa a Hudubar, ‘Duk wani jinni na jahiliyya na take shi da kafafun nan nawa, ba sauran bin bashin jinni.’ Da abubuwa masu yawa dai a cikin hudubar mai tsawo.
Amma dai haka har aka bar Arfa ba tare da Manzon Allah (S) ya ayyana musu magajinsa ba, sai aka zo Mina. Sai ga Jibrulu (AS) ya zo wajensa a Masjidul Khaib, yace masa, Ubangijinka yana gaishe ka, yana cewa ka kaddamar da Ali a matsayin Magajinka.” Sai Annabi (S) yace masa; “Ya Jibril ai min afuwa, ya zama wani ne ya yi ba ni ba.” Sai Jibrilu (AS) yace masa; “Ubangiji yace kai za ka yi, ba wani ba.” Nan Manzon Allah (S) ya yi shiru yana tunanin yadda mutanen nan za su karbi wannan abin, domin abin da ya hana shi fada a Arfa da Mina duk ya san me zai biyo baya shine za su iya bijirewa umurninsa ne, yasa bai yi ba.
Da aka gama Hajji, aka kama hanya, mutane suka kama hanya zuwa nahiyoyi daban-daban, amma mafiya yawan mutane a tafiyar da dama tafiyar yanzu, duk sukan shiga Makkah ta yamma ne.
Don a yamma akwai mahada wanda babban hanya ce, sananniya da Allah (S) ya yi maganarta a Suratul Kuraish, ita ce ta tafi har zuwa Yaman. In aka taso daga Makkah akai yamma kafin a fada ruwa akwai wannan hanyar, wacce it ace idan ta yi Arewa za ta yi har Madina ta fada har Sham, in tai Kudu za ta je Yaman. Babbar hanya ce.
Saboda haka mafi yawan mutane da suka je Hajji ta nan suka je, kuma ta nan za su koma, wadada suka zo daga kasashen yamma ko Arewa sai sun zo nan sannan suke kama hanya, haka ma ‘yan Kudu, amma wadanda suka fito daga gabas basu da bukatar su biyo wannan hanyar. Kamar wadanda suka fito daga nahiyar Irak, basu da bukatar daga Makkah sai sun zo nan sannan su kama hanya. Ko da yake a tafiyar da suna iya hakan, don a tafiyar da akan bi muhimman hanyoyi ne.
To, da aka baro Makkah akan hanya sai aya ta sauka; “Ya Ayyuhar Rasulu ballig ma unzila ilaika min Rabbika, wa in lam taf’al, fama ballagta risalatahu, Wallahu ya’asumuka minan Nas....” (Suratul Ma'ida, aya 67). Wato; “Ya kai wannan Manzo, isar da abin da aka saukar maka daga wajen Ubangijinka, in har bakai hakan nan ba kamar baka isar da sako bane.” Ma’ana, wannan abin da aka ce ka yi a Arfa, (ka baka yi ba, a Masjidul Kaib baka yi ba, yanzu an ce ka yi, in har baka yi ba tamkar baka isar da sako bane. A wata kira’ar ma; “….Fama ballagta risalatih.” Wato, kamar baka isar da duk sakonnin bane in har baka isar da wannan ba.
Wanda ya karyata Manzo daya ya karyata dukkanin Manzonni ne, haka ma wanda bai isar da sako daya ba kamar bai isar da dukkan sakonni bane. Saboda haka da Manzon Allah (S) ya ji wanna umurnin, sai ya sa maza-maza a je Mahadar nan, a tsayar da duk wanda bai wuce ba. Dama akan yada zango a wajen tukunna, kafin masu bin kudu su bi, masu arewa da yamma da gabas duk su bi hanyoyinsu. Sai Annabi (S) yace a tsai da duk wanda bai wuce nan ba. Har kuma ya iso wajen, sannan ya jira wadanda basu kariso ba suka gama isowa, aka hada masa munbari ya hau ya yi doguwar Hudubar da ake ce mata Hudubar
Ghadeer.
— Daga jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky a ranar Ghadeer shekarun
baya.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Tunatarwa