Shimfida:
Hakori wata halitta ce da Allah ya yi a cikin bakin wasu daga dabbobinsa, ciki kuwa harda mutum.Gfida:A cikin wadannan dabbobi ba bu mai kula da lafiyar hakoransu kamar mutane, don haka ne ma idan aka wayi gari mutum bai damu da wanke bakinsa ba sai ya zama kamar sauran dabbobi.
Wasu mutane ba su gane cewa; akwai hakori a bakinsu kuma yana da hakkin kulawa kamar dai sauran sassan jiki, sai lokacin da ya fara ciwo, wannan kuma ba karamin kuskure ba ne da mu ke aikatawa.
Hakan ne yasa kullum adadin masu ciwon hakora ke kara hauhawa kamar farashin man fetur a mulkin dogo dan Daura. Amma idan Allah ya so kuma ya yarda za mu yi kokarin wayarda kan al'umma domin rage yaduwar wannan ciwo.
Rashin sani abu, ke sawa a yi masa rikon sakainar kashi, a wannan rubutun namu za mu yi magana akan abubuwa kamar haka:
1. Mene ne Hakori?2. Rabe-raben hakori.3. Adadin hakori.4. Shimfidar hakori.5. Lokutan fitar hakori.6. Lokutan farfara (zubar hakori).
Da sauransu.
Mu hadu a rubutu na gaba.
Naku har kullum.-Dent FS Modibbo Gozaki-modibbogozaky@gmail.com-08063607225-07067703588-08113132445

Tags:
Cuta da Magani