Yana Daga Cikin Mafi Sharrin Mutane Ranar Alqiyama!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KADA KA KASANCE MA'ABOCIN FUSKA BIYU

Wannan abu ya zama kamar wani abin yayi a wannan zamani, duk da cewa an sami irinsu zamanin Manzon Allah (S.A.W.W ), sai dai na wannan zamani sunfi yawa.

Fuska biyu shine mutum ya kasance ya samu karbuwa wajen jinsin mutane biyu masu gaba da juna ko kuma wadanda suka sami sabani kan wani abu guda wanda yayi sanadin rabuwar kansu.

Shine wanda yake so kowanne daya daga cikin wadannan mutane biyu su yarda da shi, wanda hakan zaiyi wuya ya faru ga mutumin kirki, domin sai an sami qwarewa a munafurci kafin hakan ta samu.

Manzon Allah (S.A.W.W )na cewa;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ ZA KA SAMU DAGA CIKIN MAFI SHARRIN MUTANE WAJEN ALLAH RANAR ALQIYAMA SHINE MA'ABOCIN FUSKA BIYU, SHINE WANDA KE ZOWA WADANNAN DA WATA FUSKA , YA JEWA WADANNAN DA WATA FUSKA .‘’

A taqaice dai ana nuna mana halayyar munafuki kenan, idan kana son saurin gane irinsu maza kalli 'yan siyasar wannan zamani.

Wani abin mamaki kuma sai kaga ana samunsu cikin 'yan'uwa masu da'awar gwagwarmayar tabbatar da gaskiya da rushe qarya.

Ba zai zama abin mamaki ba ga wasu masu da'awa matuqar basu ambaci da'awarsu da sunan neman tabbatar addinin Allah na.

ALLAH YASA MU FAHINCI WANNAN NASIHA MU KUMA YI AIKI DA ITA.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

      09039791509

ASABAR , 4th July , 2020/ 14-11-1441.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post