'Yan Uwa Anya Zan Iya Wannan Tafiyar Kuwa ? hanyar ce Akwai Wuya !!!


@ Mas'udu dan Masani shinkafi

Ban son yin dogon rubutu, don haka zan isar da saqona a taqaice.
Sakamakon jarabawa da 'yan uwa suka shiga sakamakon baqin mulkin zalunci danniya da fin qarfi.Na Buhari, El-rufa'i, Da sauran Macuta Azzaluman da Suketa cuta Mana,
Har takai ga 'yan uwa suna fadin
ﻣﺘﻰ ﻧﺼﺮ ﺍﻟﻠﻪ

*"Yaushe taimakon Allah zaizo"*


Naga ya dace inyi tuni ga 'yan uwa. wadanda kuma basu sani ba Yanzu su sani.
Fatana dai mutum ya kwantar da hankalinshi ya fahinci
*haka sunnar take*
Sau da yawa zamu riqa karatun falalar bin tafarkin gidan Annabi saww kamar:-
ﻣﻦ ﻣﺎﺕ ﻋﻠﻰ ﺣﺐ ﺁﻝ ﻣﺤﻤﺪ ﻣﺎﺕ ﺷﻬﻴﺪ
*Duk wanda ya mutu akan soyayyar 'ya'yan Annabi Muhammad ya mutu shahidi*
Da irinsu tafsirin ayar nan ta suratus Saffat 24 wadda take tabbatar da bazaka wuce siradi ba sai anyi maka tambaya akan wulayar Imam Ali AS
* ﻭﻗﻔﻮﻫﻢ ﺇﻧﻬﻢ ﻣﺴﺆﻟﻮﻥ *

*ku tsaidasu lallai su abin tambaya ne*
Da irinsu Hadisin nan na Qudusi da Allah yake cewa.
* ﻭﻻﻳﺔﻋﻠﻲِّ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﺏ ﺣِﺼﻨﻲ ﻭﻣﻦ ﺩﺟﻞ ﺣﺼﻨﻲ ﺃﻣﻦ ﻣﻦ ﻋﺬﺍﺑﻲ *
*"wulayar Imam Ali as Tsari na ce duk wanda yashiga tsari na ya aminta daga azabata"*
Da irinsu Tafsirin Ayoyi biyun farko na Suratun Naba'i
* ﻋﻢ ﻳﺘﺴﺂﺀﻟﻮﻥ *
* ﻋﻦ ﺍﻧﺒﺈ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ *
*Hadisi daga Ma'aiki Ma'aiki saww cewa Wulayar Imam Ali a.s itace tambaya ta 4 cikin tambayoyin Qabari*
kuma babu wanda zai kai labari matuqar ya kasa amsawa.
Da irin su Hadisin nan da Ma'aiki yake cewa
* ﺍﻻ ﻭﻣﻦ ﻣﺎﺕ ﻋﻠﻰ ﺣﺐ ﻋﻠﻲ ﻓﺄﻧﺎ ﻛﻔﻴﻠﻪ ﺑﺎﻟﺠﻨﺔ *
*"kusaurara duk wanda ya mutu yana son Imam Ali a.s ni zan lamunce mishi shiga Aljannah"*
Da irinsu tafsirin
Suratul bayyina kan ayar
* ﺧﻴﺮ ﺍﻟﺒﺮﻳﺔ *
*Mafifitan halitta*
Inda Ma'aiki saww ya tabbatar da cewa *Imam Ali as da Shi'ar sa sune mafifitan halittu*
Da sauran dubban Ayoyi da Hadisai mara adadi da mujalladai ne.
zakuga muna jin dadi da murna muna ganin munyi dace.

To, me yasa muke mantawa da jarabawa? Da wahalhalun da wadanda mukebi sukasha?
Kar mu mantafa wadanda qur'ani ya sauka agabansu suka zauna tare da Ma'aiki saww sukaji kai tsaye daga mai tsira da aminci saww.
Amma su suka fara azabtar da 'yan Shi'a.
Mun manta Bilal yadda suka tilasta mishi barin madina?

Mun manta da Malik wanda aka tura Khalid ya yaqesu? Akace wai sunyi ridda sun hana zakka.
Aka kashesu aka maida wasu bayi, haka suka rayu cikin qunci da baqin ciki.

Mun manta Abu zarri?
Wanda daji suka mai dashi, ya mutu cikin qunci da baqin ciki.
Mun manta Ammar wanda tsinke kanshi sukayi.
Mun manta Hujr?
Da rana tsaka suka datse kanshi.
Misalan wadannan sunfi dubu.

Laifinsu kawai sunce wasiyyin Annabi saww zasubi
Kai! Bama mabiya ba, ba wani mutum daya daga gidan Annabi saww da ya rayu cikin walwala.
Tun daga Imam Ali as da Sayyida har zuwa sauran Imamai.
Ko mun mantane?
Susha baqar uquba mu musha lagwada?
Anya su mukebi?
Kar mu manta ba'a yaudaremu ba, ba'a boye mana ba.
Jagoran Shi'a na duniya ya fita haqqinmu, ya tabbatar da cewa hanyar nan
*AKWAI WUYA*
Imam Ali a.s yana cewa
*" ﺇﻥ ﺃﻣﺮﻧﺎ ﺻﻌﺐ ﻣﺴﺘﺼﻌﺐ ﻻ ﻳﻌﺮﻑ ﻛﻨﻪ ﺇﻻ ﺛﻼﺛﺔ : ﻣﻠﻚ ﻣﻘﺮﺏ،ﺃﻭﻧﺒﻲ ﻣﺮﺳﻞ،ﺃﻭﻋﺒﺪ ﺇﻣﺘﺤﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﻠﺒﻪ ﻟﻺﻳﻤﺎﻥ "*
*Lallai al'amarin mu yanada tsananin wahala, babu wanda yasan haqiqara sai uku*
*Mala'ika makusanci, Annabi Manzo, ko bawa mumini da Allah yajarabci zuciyarshi da imani*
* ﻣﻦ ﺃﺣﺒﻨﺎ ﻓﻠﻴﻌﺪﻟﻠﺒﻼﺀ ﺟﻠﺒﺎﺑﺎ *
*"Duk wanda yake son mu yayi tattalin mazubin bala'i"*
Awata fadar kuma yake cewa
* ﻣﻦ ﺃﺣﺒﻨﺎ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﻴﺖ ﻓﻠﻴﻠﺒﺲ ﻟﻠﻤﺤﻦ ﺇﻫﺎﺑﺎ *
*Duk wanda yake son mu ahlul baiti yasanya (rigar) fata (Saboda) wahala*
A wata kuma yake cewa
* ﻣﻦ ﺍﺣﺒﻨﺎ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﺒﻴﺖ ﻓﻠﻴﻌﺪ ﺍﻟﻌﺪﻭ *
*Duk wanda yakeson mu Ahlul baiti yayi tattalin (zama da) maqiya*
Zantukan sunada yawa
Tunda ko hakane ba makawa ga dukkan 'yan Shi'a suyi haqurin wahalar duniya ladanku mai kauri ne dama angaya mana garemu duniya Kurkuce.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post