HATTARA DAI 'YAN'UWA KADA JAMI'AN GWAMNATIN CIKINMU SU SAKA MU FADA IRIN TARKON DA ABU-SAFIYAN YA YIWA IMAM ALI (A.S). IMAM YA WARGAZA MAKIRCINSA
*Ma'asumah Hausa Nigerian News Updates*
*Tare da Muh'd Aliyu Daud (Dansudan) Azare.*
An ruwaito cewa bayan watsi da wasiyar Manzon Allah (s.w.a.w) na cewa Imam Ali (s.a) shine Magajinsa Halifansa a bayansa da aka yi.
Akaje Saqeefa aka yi Demokaradiyya a ka zabi wani. Wannan ita ce Demokaradiyya ta farko a duniya, Amirka ma a can suka kwafo.
Bayan wannan kwacen haqqin Imam Ali da aka yi na Halifanci, wanda ya faru a Saqeefa.
Shine bayan wannan abu ya faru Abu-Safiyan yaje ya samu Baffan Manzon Allah (s.w.a.w) wato Abbas yace dashi *"Wa 'yannan mutanen sun kwace Halifanci daga Bani-Hashim. Kai kuma Baffan Manzon Allah ne, kuma Kai Dattijo ne a cikin Quraishawa, kana kuma kyautata musu, za su karbi maganarka, muje kawai nida kai mu yiwa Ali mubai'a. Duk wanda yaja damu mu kashe shi."*
Su biyun gaba daya suka tafo wajen Imam Ali (a.s). Abu-Safiyan yace wa Imam Ali (a.s).
*"Ali, idan ka yarda zan cika Madina da Mayaqa na kasa da mayaqa na Mahaya Doki, ka karbi qudirinmu,(yana nufin a kwatowa Imam Ali (a.s) haqqinsa) kawo hanunka muyi maka bai'a"*
Da Imam Ali (a.s) ya gama sauraronsa , sai Imam ya bashi amsa da cewa:-
*"Abu-Sufiyan, Na rantse da Allah, Kai! da wannan kake so ka yi amfani ka tayar da fitina a cikin Musulmai, kullum kana ta qoqarin sai ka cutar da musulunci, bana son tausayawarka da kuma temakonka"*
*Tabari vol.iii p.202 and 303
*Taareekh Al-Kholafaa p.45
*Kanz Al-Ommaal Vol.iii p.140.
Yanzu akwai irin wannan makirci na Abu-Safiyan a cikin 'Yan'uwa a nuna cewa ana so ayi wani abu saboda kwatowa Jagora haqqinsa, amman akwai lauje cikin nadi, zahiri kuma za aga abin kamar ba komi, wato a zahiri rubutun ya yi, ko kuma maganar a zahirinta ta yi, ai neman 'yancin Jagora ne, amman a kwai makirci daga Jami'an Gwamnatin cikinmu, da zarar anyi amfani da ita kuma za ta haifar da wani abu ne marar kyau, tabbas wasu kuma a cikinmu suna temaka musu ne da sanin su ko a rashin sani. Ya kamata mu rinqa lura da kowace iriyar magana.
Hakama sai kaga mutum ya kawo maka maganar da yasan za ta haddasa fitina ne a cikin 'yan'uwa, kamar yadda Abu-Safiyan ya yi wa Imam Ali (a.s) Imam ya wargaza makircinsa, shi kuma da nufin wai nemawa jagora 'yanci, muma in munga irin wannan mu barwa mai maganar abarsa,
Wai ma ta yaya za ka nemawa Jagora 'yanci da kawo maganar da za ta raba masa kan mabiyansa, a ina ka taba ganin raba kai, da sukar wani da aibatashi a cikin addini ya zama gyara??
Da Malam kiransa da suka da aibata wasu ya fara, da duk bamu fahimci kiransa ba.
Haka kuma Malumai nawa ne suka juyawa Malam baya a wannan tafiyar, shin da aibatawa da suka 'yan'uwa suka gane su!? A'a aikin su ne ya nuna su da sannu kowa ya yi watsi da al'amarinsu.
In kana son Malam da gaske ba nufinka tarwatsa kan mabiyansa ba da haifar da fitanar da zata raba kan almajiransa ba. Toh qira za ka yi cikin hikima, ba aibata wani ko sukar wani ba.
Malam yaja mana kunne akan aibata wani da yawo da maganarsa, gashi Kai kuma kanayi toh kaga qarya kake ba neman 'yancin Jagora kake ba, raba masa kan almajiransa kake, sabida Gwamnati taji dadin kawo qarshen qiran da yake, ya zamana qarfinmu ya ragu mu shagala da juna.
Sun fada za su yi mana haka, kuma sai gashi a fili munga kanayin abinda suka fada, kaga kenan a fili kai ma'aikacinsu ne.
*Duk dan'uwan da yake sukar wani dan'uwa akan komiye toh wallahi yana yiwa jahiliyya aiki ne*
Ya yarda ko kada ya yarda, Sayyid cewa ya yi ka damu da kanka ka gyara kanka bai ce ka gyara wani ba, yace *"Gudumawar da zaka bamu a Harqannan shi ne ka gyara kanka"* inji Sayyid Zakzaky Abba.
Yawo da gulma da kawo maganar wani da baqanta wani, kowaye shi wannan komin girmansa ko qan-qantarsa yawo da maganarsa ko baqantashi ko wani abu mai kama da wannan, toh makami ne na maqiya wajen ganin bayan qiran Malam da Almajiransa. Kake temaka musu kake amfani da shi. Ka dena in bisa kuskure ne, in kuma baka dena ba munsan a Gwamnati kake yiwa aiki, kai mai rubutawa ko kuma mai yadawa ta kowace hanya, in kaqi denawa munsanka munsan kuma abinda Jahiliyya ta fi so kenan, kuma kana yi mata shi, daman ita ta baka aikin.
*'YAN'UWA MU QARA LURA DA WANNAN MAGANAR IMAM ALI (A.S) CE*
Imam Ali(a.s) yace-: "Kalamulhaq yuridul badilu biha" Fassara :- Maganar gaskiya amman ana nufin bata da ita.
Magana ce ta gaskiya amman ana nufin mummunan abu da ita, ana nufin batanci da ita ko kuma fitina da ita da makamantansu. A kwai irin wannan a yanzu a cikinmu, toh ya kamata mu rinqa lura da irinsu, kowace magana mu rinqa nazarinta sosai.
Duk maganar da za ta cire mana soyayyar juna, muna ganin wani da laifi ba abar so bace. Za ka ga anyi magana mai kyau amman ana nufin sharri ne da ita, ya kamata mu rinqa lura da irin wannan makircin ana so a raba kanmu ne a jefa gaba a tsakaninmu, a yi abinda bindiga ta gagara yi ya zama cikin sauqi sunyi ta wannan hanyar. Duk mai irin wannan rubutun raba kai ko tada fitina mu makashi mu rabu dashi ma'aikacinsu ne na Jahiliyya kuma kowaye shi duk qan-qantarsa ko girmansa.
Ka gane duk mutumin da yake nufin Harqarnan da sharri wallahi kansa zai koma ka rabu dashi, Kai gareka bai wuce wata jarrabawa ce da ake so ka tsallaketa, ba wai ka koma kana yaqarsa ba, yaqarsa bazai taba jawo alkhairi ga Harqa ba sai dai ya zame mata sharri. *Manzon Allah ya tsinewa mai tada fitin* Hakama duk wanda ya tada fitina toh shi makamashinta ne.
Ya kamata kasan cewa da ana yaqar masu bada matsalar cikin gida da an ruwaito mana cewa Manzon Allah ya yaqe su, hakama da munji Imam Ali ya yaqe su Hakama Imam Hassan ko kuma da munji Shehu Dan-Fodiyo ya yaqe su, ko kuma da munji Imam Khumain ma ya yaqe su. Duk cikin tarihi bamuji inda akace dan Gwagwarmaya yana yaqar masu bada matsalar cikin gida. Bamu ji inda aka fadi haka, shi hanqoronsa shi dan Gwagwarmaya kullum abokan gaba ne, a rubutu ko a maganarsa.
Ka tuna cewa irin wannan yanayin ne Sayyid Zakzaky (H) yaja mana kunne a kansa na kada muqi junanmu da kada mu rinqa yada maganganu da zasu jawo matsala a cikin 'Yan'uwa, har ya bamu misali da 'Yan Ik-wanul Muslim da haka aka yaqe su kuma akaci nasara a kansu.
Toh Dan'uwa mai qaunar Sayyid ka bijirewa duk mai irin wannan abun a cikin 'yan'uwa kowaye shi.
*Dan'uwa ka damu da kanka, ka kuma yiwa kowa fatan alkhairi, ka yabawa tare da addu'ar samun sabati ga masuyin abinda ya dace, ka kuma yiwa wa 'yanda suke da rauni addu'ar Allah ya qarfafe su ya ganar dasu kuskurensu, ka kuma tausaya musu, ka nema musu gafar Allah da shiriyarsa.*
Kai kuma kaji da kanka!! Don Kai kadai za a binne, kuma Hisabinka a Kai kadai za a yiwa.
In har ya zama dole sai ka yi magana. Toh ga Inda Allah yace ka yi magana. Cewa ya yi *"Udu'uu ila sabili rabbika bil-hikimati wal-mau'izatul Hasana"* Fassara:- Kai qira zuwa ga hanyar Ubangijinka da Hikima da wa'azi mai kyau.
*Free Zakzaky(H) Wa Ummuna Zeenah*
Domin sabun labaran duniya nan Gida Nigeriya dama qetare, ingantattu na kullum, tare da Sauran wasu abubuwa masu amfanarwa nayau da kullum da karatuttuka Kai har komi da komi harda abinda baka tunani ka ziyarce mu ta wannan link din👇
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Tunatarwa