Wasika Daga Gidan Yari: Mune Raunanan Bayi Sittin Da Gwamnatin Janar Buhari Take Tsare Da Mu Bisa Zalunci Tsawon Shekara Guda.



Karanta Wasiƙar Anan¶¶

Mu ne raunana da aka kashe 'yan uwan mu a gaban mu aka raunata da dama a cikin mu.

Mu ne bayin nan raunana 60 da Jami'an tsaron Buhari suka buge suka kama tun daga ranar 22 ga watan july 2019, ranar da muka fito jerin Gwano muna kira ga wannan Gwamnatin tabi umarnin Kotu ta saki Jagoran mu, tunda Babbar kotun kasa ta tabbatar zaluntar sa akayi bai yi laifin komi ba a Hukuncin da Mai shara'a Gebriel Kolawale ya yanke ranar 2/12/2016.

Mu ne bayin Allahn nan 60 da aka ciwa zarafi, aka bi ana kamawa titi-titi, lungu da saqo, tsawon kwanaki har adadin mu yakai 60

 Saboda rashin tausayi wurin masu aikata manyan laifuka da gagararrun 'yan fashi da makami dake Abuja aka ajiye mu Special Anty Robery Squad (SARS)
 aka bar mu cikin kaskanci da wulakanci,
 Wadanda aka raunata mana an bisu har Asibiti aka daukosu a lokacin da jinin jikinsu ke zuba suke cikin tsananin bukatar taimako😭.
Wasu har ansa masu ruwa wasu oxygen wasu a sume suke,
 Amma suka kwaso su suka hadamu, a gaban mu 'yan uwun mu uku suka koma ga Allah yayin da suke neman taimako koda da digon ruwa su jika makoshin su ko Audugar da za'a danne masu raunin da ke zubar da jinin jikin su amma babu mataimaki 😭
cikin wannan yanayi muke kwana a cunkushe tare da matan da ke cikin mu.
Jami'an dake tsare da mu basu yi la'akari da cewa mu ma'aboda addini bane, Addinin mu ya haramta mana haka ba.
mun shafe tsawon watanni 5 basu kaimu Kotu ba don muji laifin da muka aikata, a kasa muke kwana, abinci da magani da Sabulu sai 'Yan uwan mu sun kawo mana daga waje.



 Bayan shafe watanni 5 a SARS
Muka shigar da kara a babbar kotun kasa dake Abuja akan tsare mu da akayi ba bisa ka'ida ba, da neman Kotu ta tursasa' Yan sanda su gaggauta sakin mu saboda cikin mu akwai Daliban jami'o'i da manyan makarantu, cikin mu akwai yara yan sakandare ga kananan yara har dan shekara goma sha daya akwai cikin mu,
Sannan ga masu ciwu ka na harbin bindiga har da masu karaya.
Kafin ranar shiga kotun tayi sai sukayi sauri suka kaimu FCT High court Apo Abuja ranar 10/12/2019 suke tuhumar mu da aikata manyan laifuka 9 ciki har da kisan jami'in 'Yan sanda da kuma Dan jarida.
Shari'ar da akeyi mana a cikin gidan Yarin Kuje
Basu yarda a rika yi a harabar kotun ba, tunda basu so 'Yan jaridu da Kungiyoyin kare Hakkin bil'adama su rika zuwa suna ganin irin wainar da
Alkalin Kotun Justice Suleiman Bolaji Belgore
Da Lauyan Gwamnati DSP Simon Laugh suke toyawa.

Allah kaine gatan mu don kaine Ubangijin mu, ka shiga lamarin mu ya mafi taimakon masu taimako

12/July/2020

#WeAreTheVictimsOf22JulyAbujaMassacre.

© *_UMARY_* *_COMMISSIONER_* *_AZARE_*

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post