@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SHI FA ALLAH BA YA MANTA HALIN DA BAYINSA MUMINAI KE CIKI
Da sanin Allah aka killace Annabi Yusuf (A.S )a gidan kurkuku na tsahon shekaru 12 ba tare da an tuna dashi ba ballantana a fitar da shi.
Hakan kuwa ba yana nuna cewa Allah (T ) ya manta dashi bane ko kuma rashin sonsa ne yasa ya bar azzalumai sika cigaba da tsare shi ba, a'a, hakan ta faru ne don ya kai ajalin da Allah ya rubuta masa.
An shiga shekara ta 6 kenan azzalumar gwamnatin Buhuri wacce al'umma tayi fatan samun sauqi, 'yanci, walwala da wadata a mulkinsa ke tsare dashi tsarewa ta zalunci .
Duniya ta shaida cewa wannan bawan Allah Sayyid Zakzaky (H )an zalunce shi kuma ana kan zaluntarsa a wannan qasa me suna NIGERIA ba tare da ya taka ko zubar da kayan wani ba.
Allah mai taimakon bayinsa muminai kuma mai tozarta azzalumai ya kunyata su ta hanyar yin amfani da dokar da sukayi imani da ita wajen wanke wannan bawa nasa (H ), domin anyi shari'a daban-dabam kuma Allah na taimakonsa ta hanyar bashi gaskiya .
Duk da irin wannan taimakon da Allah ke yi masa bai sa azzalumai sun dau darasi ba saboda shaqawar da suke da ita.
Ko da azzalumai sunyi shiru kan al'amarin wannan bawan Allah , to, mu ba za muyi shiru ba. Dole ne kuma haqqi a kanmu mu fito da gangar jikinmu tare da yin rubuce-rubuce ko furtawa wajen wa'azozinmu irin wannan zalunci da gwamnatin Buhari ke yiwa jagoran muslimci Sayyid Zakzaky (H ).
Cikar ajalin Allah muke jira na ganin ranar fitowar wannan bawa nasa , domin in ya zo babu wanda ya isa ya jinkirtar da shi ballantana ya gaggautar da zuwan ranar .
‘’ LALLE AJALIN ALLAH IN YA ZO BA A JINKIRTAR DASHI KO DA SA'A 'DAYA NE, KUMA BABU MAI GAGGAUTAR DA SHI (zuwan nasa ).‘’
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Thursday, 16th July , 2020/ 25-11-1441.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
#FREE_ZAKZAKY