@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A INA KUMA YACE A FITA DASU LAYIN ZABE?
Wasu dai sun dauki yin addini ra'ayi ne da kuma ganin dama ta yadda mutum zai iya haramta abinda yaga dama ya kuma halasta abinda yaso.
Babu wani aikin addini wanda aka kebe maza da yinsa ba tare da mata ba, ko da kuwa wannan aiki ba a ce wajibi ne a kansu (matan )ba. Wannan dalili yasa duk wani aikin addini muke damawa tare da matanmu don kada aikin aikhairi ya kubuce musu.
Akan hakane wasu masu gurguwar fahinta ke yi mana kallon hadarin kaji har ma da magana ta izgilanci a kanmu saboda jahiltar addini da suka yi.
Za ka iya saurin fahintata ko gaskatani in har ka kalli yadda suke samar da fatawa kan wata manufa tasu don cimma muradin duniyarsu.
Al'amarin harkar zabe (vote )wanda malaman irin wadannan mutane ke yin wani abu wai shi (IJTIHADI )su fitar da fatawar halasta fitowar mata kan titi da layika suna gogayya da mazaje tare da yiwa junansu habaici kan wani qaton dan siyasa wanda a imaninsu suke ganin mafita a hannunsa take ba a hannun Allah .
Ba so nake na cika ku da surutu mai ma'ana ba, sai dai so nake na gamsar da ku kan abinda kuka jahilta ta hanyar taqaitattun kalmomi . Saboda haka zan bar ku da wadannan kalamai sai kuyi nazari a kansu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
Tuesday , 21st July , 2020/ 1-12-1441.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN