Wadanda Annabi(S.A.W.W )Yafi So Daga Cikin Mutane!!!


Ku Kasance Da Shafin @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @ Domin Samun Labarai, Rohotanni, Ilimiantarwa, Da Kuma warware Matsalolin Iyalin Ku dana Addini

BABU KAMAR ABUBAKAR DA 'YARSA A'ISHA IN JI BUKHARI

Da shike ni wani irin mutum ne mai wani irin tunani da wata irin fahinta, duk lokacin dana ci karo da wata magana wacce aka jinginata ga Annabi (S.A.W.W )nakan zurfafa tunani a kanta.

Manufata na zurfafa tunanin shine don na sami yaqini cikin maganar ta yadda za ta amfane ni kuma na sanar da wasu don su ma su amfana, domin da gaske akan yiwa Annabi (S.A.W.W )qarya don a fifita wani ko wasu kan wasu.

Dama amfanin hankali kenan wajen mai shi don ya tantance tsakanin gaskiya da qarya.

Allah (T )na cewa;

‘’ DON ME YASA BA ZA SU RIQA TADABBURIN ALQUR'ANI BA (ta hanyar hankalin da ya ba su ), KO KUMA DAI AKWAI RUFI NE KAN ZUKATANSU ?‘’

Wani hadisi ne da Bukhari ya riwaito da isnadi zuwa kan baban Usman , yace Amru Bn Ass ya ba shi labari cewa Annabi (S.A.W.W )ya aika shi cikin wata runduna , sai ya bi shi (daga baya )yace masa, Wanne mutum ne yafi soyuwa gare shi? Sai yace;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ A'ISHATU .‘’ Sai yace masa, daga cikin maza fa? Yace;

‘’ BABANTA .‘’ Sai yace masa, sai kuma wa (bayan su )?Yace;

‘’ SANNAN UMAR BN KHADDAB.‘’ Ya dai lissafo mazaje (da dama ina sauraronsa ).‘’

(Bukhari , hadisi me lamba 3662)

Ganin cewa ya riqa 'yarsa Fatimah da 'ya'yanta Hassan da Hussaini rasuna, wanda hakan ke nuna cewa suna raye akayi masa wannan tambaya kamar yadda Bukhari ya riwaito, sai shakkun maganar ya kama zuciyata.

Daga nan na riqa tunanin maganar tare da gwama maganganun da ya riqa yi kan Sayyidah Fatimah (S.A )da kuma Hassan da Hussaini (A.S ).

‘’ WANDA YA SANTA YA SANTA, WANDA KUMA BAI SANTA BA ITA CE FATIMAH TSOKA DAGA GANI, ABINDA YA CUTAR DA ITA YANA CUTAR DANI !‘’

‘’ WADANNAN 'YA'YAYE NANE KUMA SANYIN IDANUWA NA ‘’

Da dai sauran maganganu da ya riqa yi a kansu .

Ku taya ni nazari yaa ku 'yan'uwa musulmi da kiristoci .

Zai taba yiwuwa ga wani kamar Annabi ace ya fi son matarsa fiye da 'yarsa? Ko kuma yaso wani fiye da 'ya'yansa da 'yan'uwansa alhali wannan mutum bai fi su da wani abu ba ko da kuwa guda daya ne?

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

LITININ, 6th July , 2020/ 16-11-1441.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post