Tattaunawar Mu Da Fasto: Shin, Zai Iya Yiwuwa Ace Allah Yana Da 'Da, A Bisa Hujjar Ilimi Da Hankali??





_Tattaunawar Habibu Rabiu Nasrallah tare da pastor Barnabas._


Assalamu...warahamutul.

_KO da yake naso kawo wannan tattaunawa ne domin al'umma sukaru sukuma yi alkalanci da hankalinsu._


Duk cikar mu tsakanin musulmi da kuma a halil kitab, munyi imani da samuwar Allah da annabawasa, illah iyaka matsalar shine, wajan kadaita Allah da tsarkakeshi daga dukkan wani irin nau iyi na sharka, ta yadda anan mukayi hannun riga dasu, da kuma cikamakin annabawa, shugabana, abin koyina, gatana, haskene, abin tinkahona, wato manzan Rahama(sawa) ma"ana abul kasim mustapha Muhammad (sawa). Wanda anan aka sami banbanci tsakanin mu dasu.

KO da ya ke mafi yawan addinai akwai tushen addinin Wanda ya ginu akai, mudauki addini kiristiyanity, shi addinine da ya ginu akan samuwar Allah da kuma shi Allah yanada da, (W) kamar yadda suka kudurce hakan. Haka kuma idan muka dawo addinin musulinci addinine da ya kafu da samuwar Allah Daya tak, bashi DA abokin taraya, bashi DA da baihaifa ba akuma ba'a haifeshiba, mu barshi iya haka sakamakon na dauki wadan nan abubuwa guda biyu sabo da akansu zanyi magana.

TAMBAYAR SHINE SHIN ALLAH MADAUKAKIN SARKI ZAI IYA YIWU ACE YA NADA DA? ABISA HUJJOJI NA HANKALI DA KUMA SHI KANSA LITTAFI ME TSARKI MA'ANA BIBLE?.

Dafarko bari mufara duba akan shikansa littafi me tsarki ma'ana bible. Bible yasha banba da alkur'ani bakamar yadda mukasan alqurani haka akeba a'a da banbanci.

A matakin farko bible ankasashi gida biyu akwai tsohon alkawari da sabon alkawari.
Tsohon alkawari yana da surori 39, a inda kuma saban alkawari yake da sura 27, Wanda jimilla gaba daya surorin littafi me tsarki 66.

Baya ga haka littafi me tsarki kamar yadda suke cewa ma'ana bible Wanda mukafi Sani linjila surori 4 kacal Wanda idan ana zatan yesu almasihu yayi magana to basu wuce wadannan ba sune kamar haka:- MATTA, YOHANA, MARKUS, DA LUKE, wadannan sune iya gundarin bible hatta a wajan su kiristoci. KO da ya ke ilimi yana da fadi, kamar yadda muka tattauna da pastor Barnabas shi yace AIYUKAN MANZANIMA TANA CIKIN LINJILA, Wanda ni a iya sanina aiyukan manzani bulus shi yarabuta, KO da yake tattaunawar mu ta wakanane fuska da fuska Wanda da a rubucene na iya yankar jawabinsa. Shakka babu idan mukabi ta pastor Barnabas kunga surori 5 kenan, wannan kuma malamansu su zasu tantance, Amman azahiri kuma a yadda naji daga malumansu DA ban daban, aiyukan manzani bata daga cikin linjila, tana daga cikin rubutun bulus.


Haka kuma kamar yadda yan uwan mu kiristoci ma'ana yan uwan mu a halitta, suke dauki bible haka suke daukar alkurani Wanda sai da muka dauki lokaci me tsayi na fayyace masa yadda alkur'ani yake. Mu ta fiskancin mu musulmi alkur'ani littafine saukakke daga Allah, Wanda babu maganar wani mutum sai ta Allah tak, hatta hasalima babu maganganun manzan rahama (sawa) KO maganganun ashabul kisa, KO maganganin matansa, KO kuma maganganun wasu daga cikin zababbun sahabansa managarta, alkur'ani kafatan babu maganar kowa sai maganar Allah (T) sabanin bible, Wanda a cikinsa akwai maganganun pols, Wanda akafi Sani da bulus, KO shawulu, Wanda shi baiyi zamani da annabi isaba (as) Wanda masana tarihi sunce tsakaninsa da yesu shekaru 63, bayan dauke yesu almasihu, idan kuma mubi abin da suka fada sai muce bayan gicciye yesu. bulus ya rubuta littatfai kimanin 14 wadanda suka hadar da Timoty, kwarantiyawa, aiyukan manzanni, D.s wadanda duk suna cikin littafi me tsarki ma'ana bible, kunga sabanin alkurani Wanda shi babu maganar kowa sai ta Allah (T). Wanda da yawa kiristoci suna daukar alkurani kamar bible Wanda ba haka bane, shawarata garesu a rinka tambayar ahalin Abu aji daga bakinsu. Shine adalci.


Sabo da haka zamuyi duba abisa hankali da kuma da ilimi shin Allah zai yiwu ace yanada da (W)? Abisa Doro na hankali da Allah ya horemana a matsayinmu na yan Adam, duk wani mutum yana fatan Allah (T) yabashi da namijine Ko da macace Amman aksari shine yasamu DA namiji domin wannan Dan ya taimakamasa, a lokacin da karfinsa ya kare, domin ya tallafi rayiwarsa, ta yadda idan mukayi duba, da kyau abisa cikekken hankali, zamuka cewa duk wani Dan Adam DA yake bukatar samun DA to wannan mutumin mabukacine, ta fuska guda idan har za'a dangantawa Allah (T) DA to madalakan Allah (T) yazama mabukaci, To lallai kuwa idan Allah zai kasance mabukaci to baicika ubangijiba shi kansa da kansa mabukacine (w).


Haka zalika kuma, abisa Doro na hankali da ilimi Halitta bata haihuwar sabanin halitta, misali ba zai taba yiwu ace akuya ta hafi tinkiyaba, bazai taba yiwa ace ace kare ya haifi kuraba, bazai yiwu ace Tinkiya ta haifi akuya ba. Domin haihuwar sabanin abune da bazaiyiwuba dole sai DA asaba ta wata hanya daban. Sabo DA haka idan harko hakane, duk cikar musulimi da Krista muyarda Allah ba ya ci, bayasha, baya barci, baya gajiya, sabo da haka idan har zai yiwu ace yesu almasihi, Dan Allah ne to ko wajibine, ya siffantu da siffar uban (w) ya kasance bayaci ba yasha, baya gaciya, baya barci, domin kasantuwar yasu Dan Allah(w) zai ci zai sha, zai yi barci, to yasabawa halitta, abisa Doro na hankali wajibi ya siffantu DA wadancan suffofi na Allah (T).


haka kuma idan muka komai, abisa addinan mu, kasantuwar ba a haifi mutum babu uba sai uwa to bashi kenuna wannan mutumin Dan Allah bane, idan muka koma a addinan mu, za muga cewar, an halicci Adamu babu, uwa ba uba, ballanta yesu ya na da uwa ba, Amman babu uba, haka kuma duk cikar mu munyi amanna akan cewar Allah ya na iya yin komai, idan ya so zai Samar DA mutum Kai KO tsuntsuma KO wata dabba batare da uwa DA uba Amman sai muce wannan Dan Yayan Allah ne? Sabo DA basu DA uwa basu DA uba?.


KO DA yake shi pastor Barnabas yace dani hakane duk hakan zata kasance Amman karda na manta cewa littafinsu shine yazo da cewar yesu Dan Allah ne, kamar yadda haihuwar yesu tazo a sura matta, to tayaya zamubar abin DA littafi ya fada mubi wani Abu? Na ce da shi hakane. Shakka babu matta ita tazo DA maganar haihuwar yesu, Amman Ina da maganganu akan matta, yohana Dan zabadi, Luke, Markus, domin DA yawa idan akwai wurare DA dama acikin wadannan littafan zakaga tamkar basu suke maganar ba, Ana ba dalabarin akansu Wanda su DA Kansu akecewa sun rubuta DA Kansu.


Idan hali yayi Zan kawo wurare DA dama hakan yanuna. Cewar lallai basu suka rubutaba an rubuta DA sunansu ne.


Wassalamu.....alaikum.

©Habibu Rabiu Nasrallah.

E-mail:habibrabiu81@gmail.com

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post