@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
AHLUS-SUNNAH SUN JAHILCI HUKUNCE-HUKUNCE MASU YAWA
Sau da yawa akan halasta abubuwan da aka haramta, wani lokaci kuma a haramta abinda aka halas ta bisa jahilci ko kuma bisa son zuciya .
Tare da wannan hukunci da mutane suka hukunta ne wasu ke daga jijiyar wuya har suyi qoqarin kafirta wanda suka ga ya aikata sabanin hukuncinsu .
Yana daga cikin halastattun abubuwan da Ahlus-Sunnah suka haramta sayen amfanin gona a ajeye, abinda suke kira (fooding ).
Sunce duk wani nau'in amfanin gona wanda ake amfani da shi a matsayin abinci, sayensa a ajiye sama da kwana 40 haramunne. Sun hada da:-
Wake,
Masara,
Dawa,
Shinkafa,
Alkama,
Gero,
Maiwa/Dauro.
Suka ce, abinda ba a lissafa shi a matsayin abinci ne kadai za a iya saya a ajiye shi har zuwa lokacin da mutum yaga damar sayarwa.
Misali:-
Gyada,
Ridi,
Gurjiya/Meqoqo.
Sam wannan magana shaci-fadi ce kawai wacce ake kawowa na son zuciya amma ba shari'ar muslimci ba.
A HANKALCE
Mafi yawa hankali na tafiya da shari'a ne ba wai yadda suke cewa, ‘’ SHARI'A SABANIN HANKALI ‘’, domin Allah ya bamu hankali ne don mu riqa amfani da shi wajen gane gaskiya daga bata.
ABIN LURA :- Shi manomi mai qaramin qarfi buqatarsa shine idan aka kakace amfanin gona ya sayar ya biya buqatar da ta zama masa wajibi a kansa. Saboda haka duk lokacin da yaso sayar da amfanin gonarsa yakan zama kude yake so fiye da amfanin gonar.
Da ace zai fitar da amfanin goma sai a rasa me saye, to, cutuwa zaiyi domin zaman amfanin gonar a hannunsa ba zai amfanar da shi ba.
Shi kuma me kudi yakan taimaki manomi ne ta kowacce bangare, domin idan ya sayi kayan manomi a daidai lokacin da kudi ne buqatarsa ya taimake shi, sannan kuma idan ya fitar da shi don sayarwa a daidai lokacin da manomi ke buqata ya qara taimakonsa, domin shi manomin ya zo daidai lokacin da amfanin gonar ne yake buqata fiye da kudin nasa.
Da ace mai kudi zai qi fitar da amfanin gonar a daidai lokacin da manomi ke buqata , to, da manomin zai cutu.
Irin wannan hukunci ne ma suka fitar kan batun kudin ruwa, suka ce bayarwa da karba duk haramun ne, alhali haramcin akan me bayarwa yake.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Tursday, 28th July , 2020/ 8-12-1441.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Ahkamul islam