@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KADA KAYI BAQIN CIKIN FITAR SU DAGA TAFIYAR KU
Duk wata tafiya mai kyau Allah na tsabtaceta daga tattara shirgi marar amfani, ko da kuwa ma'abota tafiyar na tsammanin wannan shirgi/tarkace mai amfani ce gare ta.
Allah (T ) ya cika fadar Manzonsa (S.A.W.W )da munafukai marar sa adadi wadanda babu wanda yasan su sai shi (T ), amma yayi hakan ne don kada kuyi mamakin samun su cikin tafiyarku da alkhairi , domin Annabi (S.A.W.W)ma ya ci karo da su birjik.
A zamanin Annabi (S.A.W.W )Allah kan saukar da aya don ya bayyanar dasu ga Annabi (S.A.W.W ), amma baya kama sunan su sai dai alamominsu wanda za a iya gani asan cewa sune don a nisanci aikinsu. Amma yanzu babu aya sai dai a gane su ta hanyar zantukansi da ayyikansu kamar yadda Uma Bn Khaddab yace.
Allah (T )ya bayyanar mana da alamominsu inda yake cewa;‘’ ZA KA IYA GANE SU TA HANYAR TUNTUBEN HARSHE .‘’
Ma'ana za ka ji maganganunsu na sassabawa da juna, wato ana samun cin karo cikinsu .
Sannan Annabi (S.A.W.W )ya kawo alamominsu, daga ciki yake cewa idan husuma ta shiga tsakaninku sukan fajirce. Wato ko da anyi zama da su don fahintar juna sai su kangare su qi yarda da wannan sulhun.
To, su wadannan babu alkhairi cikin tafiya gare su a kowanne irin lamari.
Allah (T )yayi bayanin haka inda yake cewa Annabi ;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ DA SUN FITA A CIKINKU (zuwa yaqi )BA ZA SU QARE KI DA KOMAI BA FACE DA BARNA, KUMA LALLE DA SUN YI GAGGAWAR SANYA ANNAMIMANCI A TSAKANINKU (don su raba kanku ) , SUNA NEMA MUKU FITINA (cikin tafiyar taku.)KUMA A CIKINKU AKWAI 'YAN RAHOTO (masu daukar sirrinku suna bayanar da shi )SABODA KU. KUMA ALLAH NE MASANI GA AZZALUMAI .‘’
(Tauba, aya ta 47)
Saboda haka kasancewar su cikin tafiyarku babu alkhairi , fitar su shine mafi alkhairi .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Wednesday , 15th July , 2020/ 24-11-1441.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
#FREE_ZAKZAKY