@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KU NISANCI ABUBUWA DA YAWA NA DAGA ZATO
Saboda nemar mana da mutuncinmu da kuma nisantarmu daga aikata abinda zai iya kaimu ga halaka yasa Annabi (S.A.W.W )ya hane mu game da yin zato ko aiki da shi .
Yin zato kan kai mutum ga halaka, domin yakan sa mutun ya fassara dan'uwansa da wani sharri cikin ayyukansa na alkhairi , kuma yakan sa a cutar da mutum ba bisa haqqi ba.
Manzon Allah (S.A.W.W )na cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ NA HANE KU DA YIN ZATO, DOMIN ZATO ZANCEN QARYA NE (don ba shi da tabbas ), KUMA KADA KUYI BINCIKE (na shan qwaqqwafi cikin abinda bai shafe ku ba ), KUMA KADA KU KASANCE MASU YADA (broadcasting )MAGANA (ta sharri ko wacce ba ku da tabbas cikinta ), KUMA KADA KUYI HASSADA (ga wani don kunga Allah ya fifita shi da wani abu , ilimi ne ko dukiya ko kuma wata daukaka daga Allah ), KUMA KADA KU JUYA BAYA (ga 'yan'uwanku ku maida su abokan gaba gare ku ), KUMA KADA KUYI FUSHI (da wani wanda hakan zai hana ku aikata wani alkhairi gare shi ku yi masa fatan sharri ), KU KASANCE BAYIN ALLAH 'YAN'UWAN JUNA (masu qaunar junansu da yiwa juna fatan alkhairi ).‘’
(Bukhari, hadisi me lamba 6065)
Wannan babban qalubale ne ga musulmi masu fassara 'yan'uwansu da wata mummuniyar manufa don cimma wata boyayyiyar manufa .
Kuma wannan hadisi na fassara ayar nan da ke cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI !KU NISANCI ABUBUWA MASU YAWA NA DAGA ZATO, DOMIN SASHEN ZATO ZUNUBI NE........‘’
(Hujrat, aya ta 12).
‘’ KUYI TADABBURI YAA KU MA'ABOTA HANKALI .‘’
Daga wakilanmu na B auchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
ASABAR, 4th July , 2020/ 14-11-1441.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Tunatarwa