Maganar Gwamnati Na Bani Kudi Ba Gaskiya Bane – Inji Sheikh Yaqub Yahya Katsina



- Daga Bin Yaqoub Katsina

Wakilin ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky (H) na Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya Katsina, ya bayyana hakan a yau Juma’a 10-07-2020 kafin fara karatun sati-sati da ke gudana a Markaz.

Da yake bayani Malamin ya bayyana cewa lallai maganar kudin da aka ce an bashi ba gaskiya bane, kuma yana ci gaba da daukar matakan da ya dace kan gano yadda akayi kulla-kullar. Ya bayyana cewa ya nemi da shi Mahadi Shehu ya bada ‘Copy’ din ‘document’ (takardun shaida) da yace sune suka madogararsa domin mai yiwuwa akwai ko akwai masu amfani da sunan sa suna karban kudi a tunaninsu ba zata tonu ba. Amma dai Mahadin ya hana takardun, yace ‘sai dai a hadu kotu’.

Malam Yakubu yace; nan ne ya gane lallai akwai wani abun, amma yace ya damka lamarin hannun lauyoyi subi su ga yadda za a iya amsar ‘Document’ din, in hakan ta gagara to mai yiwuwa sai anje kotun ta karbar masa, ya danganta ga yadda lauyoyin suka ce.

Shaikh Yakubu ya ja hankalin Mahadi Shehu da gwamnati tare da sauran duk wadanda ake zargi da karbar kudaden cewa; su sani duk abinda mutum yayi ko ya dauka da-dai da allurar ta kudin jama’a zai bada bayani gaban Allah gobe kiyama. Shi kuma Mahdi ya gane tunda yace yana yin nasiha ne ko za a gyara, to in har nasiha ne ba haka Annabi (S) Yace ayi nasiha ba, a kebance Annabi Yace.

Tun da farko Shaikh Sai da ya fara bada tarihin irin yadda tun can baya shekarun da suka gabata an masa tayin karbar kudade kala-kala amma bai karba ba, yace ko shekara biyu da ta gabata wani daga Abuja ya aiko masa da kudi Naira miliyan biyu, amma ban karba nace a koma masa da kayansa, ‘shi zai mani shaida in yaji wannan maganar’ in ji Shaikh Yakubu.

Mu tarbiyyar da Sayyid Zakzaky (H) ya bamu ba hadafimu kenan ba duk da muna da bukatoci kuma da kudi ake yinsu amma mun zabi mu fitar da Addini kunyar da Malamai suka saka shi ko da zamu zauna cikin talauci. Yana daga baiwar da Allah ya bani shi ne ba wata bukata da ta zamar mani dole, wadda in banyi ba zan shiga matsala, a’a in ta samu ayi in bata samu ba kuma shi ke nan. Yace akwai abubuwa da dama da yake dasu kasa zai fada amma zai tsaya haka in aka ci gaba to zai ida fadar sauran.

Daga karshe Shaikh Yakubu yace; duk wanda ya zarge shi ya sani ko bai sani ba shi ya yafe masa, wanda kuma ya ke yi da gangan to wannan kuma shi da Allah…

In ba'a manta ba dai cikin satin da ya gabata dai wani Mai suna Mahdi Shehu ya bayyana a kafar sadarwa ya bayyana wasu kudade da yace an baiwa mutane daban daban cikin kudin tsaro da aka baiwa jahar Katsina, inda har ya ambata Malamai Ukku daga ciki hada Shaikh Yakubu Yahya Katsina yace an basu makudan Miliyoyi...

@MediaForumKatsina

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post