Shafin Ma'asumah Ba Zai Taba Tozarta Ba!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SHEIKH YA'AQUB YAHYA NE YA GYARA WANNAN SUNA

Kamar dai yadda masu bibiyarmu suka sani, wannan shafi an gina shi musamman don isar da saqon Allah (T )qarqashin jagoranci da karantarwar Sayyid Zakzaky (H ).

Tare da wannan manufa ne kuma aka shigar da kawo rahotanni na kowanne fanni da sauran ilimomi daga kowanne bangare. Duk mai bibiyarmu zai gaskatamu kan wannan magana matuqar yana binmu ne da budaddiyar zuciya mai dauke da alkhairi .

Ga wadanda suka dade tare damu sun san wannan shafi ne da suna MA'ASUMIYYAH ba MA'ASUMAH kamar yadda kuke ganinmu a yanzu haka ba.

Wannan canjin suna ya biyo bayan wani Mu'utamar ne da muka yi a Katsina wanda muka sami albarka da fatan alkhairi daga bakin Sheikh Ya'aqub Yahya.

Bayan gabatar da kanmu gare shi tare ambaton garin da kowa ya fito daga cikinmu, kuma jagoran wannan shafi (FOUNDER )yayi masa bayani kan manufar samar da wannan shafi , sai Sheikh yayi farin ciki da jin wannan kyakkyawar manufa .

Yayi mana nasiha sosai kan riqo da wannan harka tare da aikata abinda jagora S ayyid (H )zai yi farin ciki da shi, da kuma nisantar aikata duk wani abu wanda zai iya cutar da haka islamiyyah wacce Sayyid (H )ke jagoranta.

Jin wannam suna da muka ambaci shafinmu da shi shine Sheikh yace da za mu ambaci shafin da suna MA'ASUMAH maimakon MA'ASUMIYYAH zai fi bada ma'ana. Kuma ya fada mana dalili kan gyara wannan suna .

Tun daga wannan rana mu kayi ta qoqarin koyawa kanmu ambaton wannan suna sabanin wanda muka saba da shi. Bayan wannan lokaci ne aka dawo kan wannan suna MA'ASUMAH .

Tabbas, muna fahari da samun wannan canjin suna mai ma'ana fiye dana farko. Kuma muna da kyakkyawan fatan cin albarkacin bayin Allah da su kayi mana wannan gyara, da kuma albarkar mai sunan.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

Thursday 16th July, 2020/ 25-11-1441.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post