Sallah Na Gaba Da Ci, Ko Dai Ci Na Gaba Da Sallah???




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Annabi (S.A.W.W )ya ambaci sallah da suna ginshiqin addini , wanda ya tsaida ita ya tsaida addini , wanda ya tozartata kuma ya tozarta addini .

Ta kasance ibada mai girma wacce ko a fagen yaqi ake ba a sassauci a kanta, hakama jinya ba ta sa sallah ta fadi a kan mutum, domin akan ramata bayan samun sauqi ga marar lafiya.

Shi kuma abinci na cikin babi ne na abubuwan da aka halatta su, ba wai bisa babi na wajibci ba, saboda haka za ka iya ci in kana da buqata , in kuwa babu za ka iya zama babu ci kuma babu mai zarginka kan haka.

Na'am, abinci na da amfani ko ya zama lalura mutum yaci, domin babu rayuwa in babu ci, kuma hatta ibada bata yiwuwa in babu ci.

Tare da wannan nazariyya biyu wasu ke cewa sallah na gaba da ci, domin ita wajiba ce akan bayi, kuma tana da lokaci qayyadajje.

Sai dai kuma an sami wani hadisi cikin Bukhari inda yake cewa;

Mu'allah Bn Asadin ya bamu labari , Wuhaibu ya bamu labari daga Ayuba, daga baban Qilabata, daga Anas Bn Malik , daga Annabi (S.A.W .W )yace;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ IDAN AKA AJIYE ABINCI (domin aci ), KUMA AKA TSAIDA SALLAH (aka yi kira ko iqama ), TO, KU FARA DA ABINCIN .‘’

(Bukhari , hadisi me lamba 5463)

A wata riwaya kuma aka ce,

‘’ IBN UMAR KUWA YA CI ABINCI SAU 'DAYA YANA JIN KARATUN LIMAN .‘’

(Bukhari , hadisi me lamba 5464)

Shi yasa na yiwa wannan rubutu kanu da cewa,

SALLAH NA GABA DA CI KO DAI CI NA GABA DA SALLAH?

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

      09039791509

Monday, 27th July, 2020/ 7-12-1441.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post