Sako muhimmi zuwaga yan'uwa Almajiran Sayyid Zakzaky (H) -Daga: Shaikh Yakubu Yahaya Katsina.

DUK DAN'UWAN DA YA AMSA KIRAN SHAIKH ZAKZAKY (H) AKWAI FATAR LAYYA 1 A KANSA - Shaikh Yakubu Yahaya Katsina.

Daga: Bin Yaqoub Katsina.

Jiya Alhamis ne 26 ga Zulqida, 1441 16/07/2020 Shaikh Yakubu Yahya Katsina yayi wannan kira bayan ida karatun Tafeer da akayi a duk ranar Ta'alim a Markaz Katsina.

Malamin ya ja hankalin 'yan'uwa da su dage wajan sauke nauyin iyalan shahidai da tallafawa da fatar layya guda 1 ga dukkan dan'uwa da amsa kiran Shaikh Zakzaky (H) musamman yadda Sallar layya ke kusantuwwa.

Yace ba laifi ga dan'uwa da dan'uwa su hada kudi su sayi rago suyi layya (mu a mazahar Ahlulbaiti,  wadan da sune aka saukar  da addinin a gidansu), maimakon tantan da wasu ke yi, yin wancan hadakan zai taimaka wajan ba da fatar layya ga Mu'assasatu Shuhada sannan ga ladar layya, riba biyu.

Sannan Shaikh Yakubu ya cigaba da cewa lallai ya wajaba ga dukkan wani dan harka buraza da sista su bada fatar layya guda-guda ko da basu yi layya ba su saya su bada. Ko kuma naira dari biyar a madadin fatar. "Na san dai daga nan zuwa Sallah Allah ba zai hana mutum dari biyar ba" Inji Shaikh Yakubu Yahya Katsina...

Daga karshe ya kara karfafa lallai hakki ne dole mune zamu sauke amma kada kuma ka dauko na wani in bai bada ba, a  tamaya kafin a karba ko da wajan makwabcinka ne, kayi masa bayani in zai gamsu kuma ya tallafa.

@MediaForumKatsina
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post