Malamin da ya samu Shaidar Imani da Yak'ini.
...
Ta yaya zan bar shi na bi Mai Siffar Columbus ..Mai Tafiya bincike bincike.....
.....
(Christopher Columbus 1451 – 20 May 1506) was an Italian explorer, navigator, and colonizer. )
.....
Lokacin da Columbus ya fara tafiyar binciken sa.. bai San inda zashi ba.. Da ya Isa gurin bai san a inda yake ba ..Da kuma ya dawo gida , bai san Inda ya je ba.
....
To ina kaga labari idan kabi mai Wannan Siffofin da sunan jagora ?????
...
..
Ni nawa Malamin kuma jagora shine wanda "Makiyin sa na Yanzu Almajirin sa a da.. yayi wa Wannan Shaidar ....
kamar haka.
...
1— "Malam Ibraheem Zakzaky wani mutum ne wanda yake yana da hadafi, sannan kuma ya fahimci hadafin nashi 100%, kuma yana da yakini akan hadafin nashi...
2— "Hadafin nashi (kamar yadda ni na fahimta) shine dawo da mutane izuwa ga bin Allah (T), kamar yadda Allah ke cewa dangane da Manzonin da ya aiko; "Su ne wadannan wadanda suke isar da sakon Allah (SWT) (Manzonni kenan), sannan suna Jin tsoron Allah (T) din, sannan kuma basa Jin tsoron kowa a cikin Duniyar nan idan ba shi Allah (T) din ba.... Kamar yadda ya zo a Hadisi Manzon Allah (S) yana cewa: "Madalla da mutumin da tsoron Allah ya shagaltar da shi daga tsoron mutane." Wannan Shine hadafin Malam Zakzaky; Wato isar da sakon Allah (T) tare da Jin tsoron shi da kuma kin Jin tsoron wani da Ba Allah (SWT) ba.... Wannan kuma shine hadafin dukkan Manzonin Allah baki dayansu....
3— Hadafin Malam (Zakzaky) a takaice shine mai da mutane zuwa ga Allah (T) wanda yake shine Ubangijinsu. Sannan kuma wannan aiki din shine ainihin aikin kowane daga cikin Manzonin da Allah (SWT) ya aiko su zuwa ga mutane daga lokaci zuwa lokaci har zuwa lokacin Manzon Allah Muhammad (S)...
4— Ina cewa kuma yana da yakini akan hadafin nashi.... Akwai lokacin da muka taba tafiya Jaula a Gombe a 1990, sai Malam Zakzaky ya yi Wa'azi, a ciki yana nuna cewa Tabbas addinin Allah (SWT) sai ya tabbata, yana da yakini akan hakan. Lokacin da aka gama Wa'azin da muka koma gida haka, sai nace mishi, me yasa yace yana da yakini dole ne addinin Allah (T) sai ya tabbata? Sai yace min wannan alkawarin Allah ne a cikin Alkur'ani, a suratul Nurr, Allah ya ma wadanda suka yi imani suka yi aiki na gari, cewa zai kallafa su kamar yadda ya kallafa wadanda suka gabace su. Saboda haka daga wannan ayar yake da yakini akan cewa tabbas Allah (T) zai tabbatar da addini a doron kasa. Ko da wadanne irin mutane ne....
5— "Duk mutumin da ya ga 'suluk' din (Malam Zakzaky), da yadda yake tafiyar da al'amarin da'awarsa, zai samu irin fahimtar da nake da shi na cewa (Malam Zakzaky) yana da yakini akan abin da yake kira. Wato daidai ne a tashi a yi kira ga mutane su koma ga Allah (T) wanda Shi ne mahaliccinsu....
6— "...A kan haka ne Malam Zakzaky ya ginu, shi yasa ma ya zama ba shi da tsoro (kamar yadda Annabawa suke) a kan isar da wannan sakon na Allah (SWT), ko me zai faru baya tsoro.... (Malam Zakzaky) yake cewa; "Nasara gare mu ita ce mu fadi gaskiya sannan mu yi aiki da ita wannan gaskiya din da muka fadi, Nasara a wurinmu ba ita ce yawan Mutanen da suka karbi abin da muke cewa ba. Ba kuma ita ce tabbatar addini a hannunmu ba.... Saboda haka baya Jin tsoron tafiya a kan wannan hadafin da ya tsaya a kansa. Baya tsoron duk abin da zai faru.
........".
....
....
LABBAIKA YA ELZAKZAKY H.
...
#AllahProtectZakzakyH
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Jagoran Gaskiya