Na Kanji Babu Dadi Matuqa, Naga Wasu Daga Cikin Yan Shi'a Musamman Mabiya Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Suna Zagin Wadansu Daga Cikin Wadanda Suka Zauna Da Annabi (s.a.w.w) – Inji Habibu Rabiu Nasrallah



Yawaitar maganganu na zaki, da izgilanci ga wadansu da suke raya cewar, su yan shi'ane kuma almajiran allama zakzaky, abin ban takaici ne, asamu almajirin Malam ya na zagin wasu daga cikin wadanda suka zauna da annabi, wala acikin matansa (sawa) ko wadanda suka zauna da shi a matsayin sahabbai.

Ta yadda abin yayi kamari idan kaduba shafin Facebook, hakan shi ke nuna cewar wasu har yau basu fahimci kiran sayyid ba, abin ban takaice, da bacin rai, zakatar suna jazawa aimma zaki DA aibatawa, Kai hasalima har ashabul kisa'i ba abarsuba zaka Tatar wasu na tabawa, kuma, badan komai ba sakamakon zagin gwarazansu. Har yaushene shi'aci yazama zagi? Har yaushene kiran sayyid zakzaky ya koyar da zaki da cin mutumcin wasu DA ga sahabbai?

Lallai wannan kuskurene, hankoran mu da fatan mu al'umma sugane wasiyar da annabi yayi a dawo kanta, bai koyar da mu zagiba, hasalima imam Ali yanacewa kar Ku kasance masu zagi, Amman Ku kasance masu, fadar abin da suka aikata........ Haka zalika, akwai wani malami akasar nan da ya taba kawai sayyid zakzaky ziyara suka tattauna daga ciki ya ke cewa idan har kasamu wani dagacikin mabiyana suna zagin sahabbai to kugayamana mukuma zakuga yadda zamuyi da shi, a lokacin da halluru maraya ya kaiwa malam ziyara.



Sabo da haka al'umma ya kamata kufahimci mu da kyau ako Ina Ana samun bara gurbi, zakin wasu daga cikin sahabbai ba koyarwar malaman shi"abane, haka kuma ba shi ancibane, bugu da Kari bakoyarwar Malam zakzaki bane.


kirana ga wadanda suke da wannan Dabi'a ya kamata kuji tsoran Allah kar kufitini al'Umma, fatan mu har kulum al'um mar musulmi su fahimci hakikanin addininsu, su fahimci wasiccin manzan rahama (sawa), ina ribarka nayin zagi ga wasu matattatu,? Kasance me magana da hikima ta hanyar buda tunanin mutane su gane gaskiya, ba ta hanyar wargaza tunanin su, wani da ga cikin a imma yanace cewa Ku kasance masu Kira da hikima da kuma kyawawan dabiu...

Amman zaki banaka bane, cinfiska, banakabane, Amman katsaya kyam ka fahimtar da mutane wasiccin annabi ta KO wacce siga wannan ba laifibane, fadawa duniya irin zalincin DA akayiwa Yayan annabi ba laifibane, Amman zaki wannan aikin wawayene, Ina ribarka, ka zagi gwarazan wasu, an zaki a imma, wacce riba kasamu?

Wassalamu....war ah am.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post