Mu Nisanci Cutar Da Maluman Mu Ta Hanyar Yawaita Tambayoyi!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SUN CUTAR DA ANNABI (S.A.W.W )TA HANYAR TAMBAYOYINSU

Ba hikima bace ko qwarewa ko burgewa ace don malami ya gabatar da wata (lecture )ko wa'azi a riqa yawaita masa yin tambayoyi .

Babu laifi a taqaita musu tambayoyi masu ma'ana ko da kuwa shi ya bade qofar yin tambayoyin ta hanyar bada umarni ko nema.

Haka ta faru a zamanin Manzon Allah (S.A.W.W )har ransa ya baci yadda aka gano a fuskarsa, amma bai fasa cewa a tambaye shi ba.

Bukhari ya riwaito daga Yusuf Bn Musa yace, baban Umamata ya bamu labari daga Buraidi Bn Abiy Burdata, daga baban Burdata, daga baban Musa Al-Ash'ariy yace; An tambayi Manzon Allah (S.A.W.W )abubuwa wadanda basu dace ba, yayin da tambayoyin suka yi yawa gare shi sai ya fusata, yace;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ KU TAMBAYE NI .‘’

Sai wani mutum ya miqe yace, ‘’ Yaa M a'aikin Allah ! Wanene babana?Yace:

‘’ BABANKA SHINE HUZAIFATA .‘’

Sa'an nan wani ma ya miqe ya qara cewa, Yaa Ma'aikin Allah ! Wanene babana? Yace;

‘’ BABANKA SHINE SALEEM MAULA SHAIBATA .‘’

Abu Musa Al-Ash'ariy yace, yayin da Umar yaga abinda ke fuskar Manzon Allah (S.A.W.W )na fushi, sai yace,

‘’ LALLE MUNA TUBA ZUWA GA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA (kan irin wadannan tambayoyi masu cutar da Annabi ).‘’

(Bukhari , hadisi me lamba 7291)

Yanzu dan Allah menene amfanin irin wadannan tambayoyi ga masu yinsu ko ga masu saurare?

To, har yanzu za ka ji ana yiwa maluma irin wadannan tambayoyi marar sa ma'ana da amfanarwa a guraren programmes . Pls, a kiyaye.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

ALAMIS, 2nd July, 2020/ 13-11-1441

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post