Menene mahangar Muslunci dangane da soyayya??

MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATED

-Menene mahangar Muslunci dangane da soyayya tsakanin jinsi guda biyu (Namiji da Mace)?


-Wani abu ne da Shari'a ta yarda dashi, musamman in muka ga zai iya faruwa ba tare da bin munanan hanyoyi ba. Muslunci yana son dukkan ɗan Adam mace/Namiji ya zam yana da fahimta mai kyau akan soyayyarƴ  Wanda aka bawa kowa damar yaji yana son ɗan uwansa, wanda ta haka ne ke haɗa kan mutanen ta ɓangaren ƴan Adamtaka.

-Wanda ya haɗa da bada kulawa, kariya, kula da bukatu, daraja mutum, da girmama manya da sauransu. Haka, kuma munga cewa; Manzon Allah (S) yana alaƙanta Imani da So. Kamar yadda ya faɗa: "Imanin ɗayanku baya cika harsai ya soma ɗan uwansa abinda yake soma kansa, ya kuma ƙi wa ɗan uwansa abinda yake ƙiwa kansa".

-Wannan yasa muka fahimci yadda Hadisai suka nanata mana yadda ake nunawa dajin abu akanka da yadda zakaji ga ɗan uwanka. Sabida haka, kai ba cikakkaen mai Imani bane in ya zama kana kallon wasu ba komi ba, ka kuma barranta musu, ba tare dajin wani abu game da lamarinsu ba. Mun gani a wani sanannen Hadisi cewa; "Duk wanda bai damu da al'amuran Musulmi ba, toshi ba Musulmi bane".

-Abin nufi anan mutum dole yaso ɗan uwansa a ƴan Adamce. Yazo a wani Hadisi da aka tambayi Imam game da So. Imam As-Sadiƙ (As) yake cewa, "Ai addini dama wani abu ne baya ga So?" Don haka wannan shine kawai, a cikin rabe-rabensa dan gane da ƴan Adamtaka. Amma akwai wani abu a tattare da mutum wanda ke ingiza shi yaso wani kamar yadda yakeson abincinsa da abinshansa.

-Soyayyarsa tana tahowa ne 'direct' sabida banbancin jinsi takaisa da son ɗayan jinsin nasa, hakan shine abinda yawancin matasanmu ke fiskanta lokacin samartaka. Da ɗaukar hankalinsu ga kyawun jiki, aikata Jima'i, da sauransu. Mun fahimci Muslunci yana buƙatar ɗan Adam (Mace/Namiji) ya gane wannan so ɗin ta yadda Soyyarsa zata zam kammalalliya. Babu wani ƙin yarda da akayi Namiji yaso Mace, ta yin sha'awar kyawunta, da son ya aureta. Muslunci ya yarda mutum ya kalli macen da yake so ya aura, domin bayyana soyayyarsa da shirya tsare-tsaren da zasuyi a zaman gaba ko abinda yai kama da haka.

-Duk da haka, Soyayya wacce take ta wasa, cin mana, ko wacce ake aikata ayyukan da suka saɓawa shari'a, haramun ne a Muslunci. Kai, dukkan abu da ya zam zai kai ga aikata zina, koda daga zuciya, harshe, ido, hannu, ko wasu sassa, kai koma menene indai zaikai ka ga hanyar zina, koda shiryayye ne, yakaika ga zuwa son aikatawa, ya kau a Muslunci. Yakan kai mutum ga aikata aikin haram, wanda ke nesanta bawa daga bin umarni Allah maɗaukakin sarki.

-Idan muka kalli soyayya irinta hauka da wasu keyi, ba tare da son rai ba zamu iya kawo wasu shawarwari da za'a samu dacewa, domin Allah baya tilastawa bawa wani abu da bazai iya ba kuma bai kawo masa abinda ya fice tunaninsa. Muslunci yana son muzam masu iya tasarrufin zuciyoyinmu, ba tare da sun zama masu ingizamu ba, mu zama masu tunani, ta fuskacin kiyaye son ranmu. Mu zama masu zurfin tunani, da ƙoƙarin kare zuciyoyin mu ba tare da tafiyar da ayyukanmu wawii ba, Muslunci ba ya kawo wannan bane kawai domin neman abokan zaman aure, a'a saidai ga dukkan abota.

-A kuma ɗayan bangaren, Muslunci ya kawo waɗannan ne don kariya garemu, badon mu sami damar keɓewa mu kadai ba. Ba kuma ya bamu damar bayyana so bane ta hanyar runguma ko wani abu da suka gabata a baya ba. Kuma Muslunci bai hana wasu maganganu na bayyana Soyayyaba, matukar basu ci karo da abinda shari'a tazo dashi ba.

Wasallallahu ala Muhammad wa alihiɗ ɗahireen.
____
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post