HOTO DAGA ABNA24.COM SOURCE: ANBA24.COM |
Wakilan gamayyar jam’iyyun “Fath” a majalisar dokokin kasar Iraqi sun bukaci gwamnatin Mustafa Al-Kazimi ta gaggauta shigar da karan Amurka a hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya dangane da kissan Abu Mahdi Almuhandis a farkon wannan shekara.
Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya bayyana cewa wakilan gamayyar jam’iyyun sun bukaci a kafa kwamiti na musamman wanda zai rika bin duddugin inda aka kwana kan shigar da karar.
Daga karshe majalisar dokokin kasar ta Iraqi ta yaba da yin allawadai da hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya ta yi na kashe Janar Qasim Sulaimani wanda gwamnatin kasar Amurka ta yi a farkon wannan shekara.
A ranar 3 ga watan Jenerun wannan shekara ne dai, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada umurnin kashe Janar Kasim Sulaimani kwamandan rundunar Qudus ta JMI tare da Abu Mahdi Almuhandis da kuma wasu mutane 8 tare da su a tashar jiragen sama na birnin Bagdaza na kasar Iraqi.
SOURCE: (ABNA24.com)
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :
MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
Tags:
Labaran Duniya