Ana diga ma yaro maganin rigakafin kamuwa da cutar shan inna, Polio.
Dr. Lawal Aliyu Rabe, darektan Kiwon lafiya daga tushe a Jihar Katsina, yayi bayanin yadda a Hausance aka samu kalmar rigakafi da kuma dalilin da ake yinsa.
Darektan kula da lafiya tun daga matakin farko a jihar katsina, Dr. Lawal Aliyu Rabe, ya bayyana cewa Hausawa sun sanya ma hanyar kare jiki daga kamuwa daga cututtuka sunan rigakafi ne, domin nuna yadda ake sanya magani ya "riga" cuta shiga jikin mutum domin yin "kafi" ko mamaye wurin da cutar zata nemi kamawa.
Dr. Rabe yace ana ce "rigakafi" ne domin bayyana wanda ya riga yin kafi a tsakanin cutar da kuma magani, domin wadansu cututtukan su na da wuyar yin magani idan sun riga yin kafi a jikin mutum.
Kwararren likitan, wanda yayi magana a zauren taron yaki da cutar Polio da Muryar amurka ta gudanar kwanakin baya a garin Katsina, yace yawancin ana yin rigakafin ne domin cututtuka irinsu shan inna ko Polio, watau cututtukan da kwayar cuta mai suna Virus take haddasawa.
Amma kuma yace akwai wasu cututtukan da wasu kwayoyin cutar ma suke haddasawa, kamar cutar nan ta tarin fuka wadda yace ita ba Virus ce ke haddasawa ba.
Amincin allah Yatabbata agareku maabota shiriya da wulaya,
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Cuta da Magani