Likita_Shin Fara Zubar Jini Ga Yarinya Qarama Me Shekara 12 Zuwa 14 Ciwo ne ko Al'ada ce ??



MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATED


Daga Alkalamin: Arrida Chemist💊Shinkafi

Amsa :

Wannan Babu wata matsala Kuma ba Ciwo bane.
A addinance ma yar shekara tara 9 akace mana ta balaga.
kawai ya dangantane da yanda Allah yayi ko wacce macce da irin halittarta
Wanda kuma wani lokaci samun isashen hutu da cin abinci me Gina jiki na daya daga cikin abunda ke sanya wata tsoka dake cikin jiki Wanda Takeda suna (estrogen hormones)
yafara aiki yanda yakamata har yarinya
tafara jinin al' ada hasalima bawani
bakon abubane saudayawa ake samun
hakan yar shekara 12 ko yar 13 tayi jinin Al' ada
Musamman qasashen qetare da zakaga babban mutum har da gemu amma shekarunsa ba yawa.
Amma lalle mukam A Nigeria da azzaluman shugabanni sun talauta mutane to yarinya yar shekara 12 karamace sosai saidai qalilan

ALAMOMIN BALAGAR YA MACCE WATO
(PUBERTY)

1.yin jinin. al' ada
2.fitowar gashi a mararta
3.fitowar nono
4.Budewar muryarta takoma babba
5.fara gashin hamata

Zata iya daukar ci idan tafara jinin
Al' ADA WATO PERIOD
abubuwa da dama kesa hakan
idan estrogen hormones da progesterone suna samun abunda sukeso daga jikin ya maccce WATO abinci me Gina jiki lafiyayyen abinci sannan yarinya tana samun koshi a koda yaushe lalle babu makawa zata iya samun yin AL' ada tanada shekara 12 ko 14 wannan yanada nasaba da yanayin yanda Allah ya hallici cell din kowacce ya macce lokacin da (estrogen hormones) idan yasamu abincin me Gina jiki da Karin lafiya da samun isashen hutu ga yarinya
to a lokacin ne yarinya wasu tsokokin
jinkinta zasu Kara girma saboda samuwar
abunda jiki keso hartakaiga tayi saurin
balaga dafara jinin Al' Ada
abubuwanda ke karama jiki lafiya da
sanya (estrogen hormones) samun yin aiki yanda yakamata sune:

1.banana ayba
2.orange lemu
3.meat nama
4.fish kifi
5.milk Madara
6.vebrages
7.calcium
da sauransu

TO MIYAKAMATA MATA UWAYEN YARA
YADACE SUYI GA YAYANSU MASU
KANAN SHEKARU DA SUKAFARA AL' ADA

1. kizaunarda yarinya kifadamata sirrin
komai kuma ki kwantarmata da hankali
2.kikoyamata wanka bayan gama AL
ada a addinance
3.sannan ki koyamata tsafta da koyamata
saka always pad da canzawa Saboda gujema kamuwa da cutuka (infection) Saboda kazantama tana sanya infection
4.ki fadamata da koyamata yanda zata
rinqa hankuri da ciwon Mara lokacin AL' ada da kuma kara kiyayeta Saboda a lokacin zata iya daukan ciki.

Allah yabaku lada Iyayenmu mata

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post