Fira ministan Labanon, Hassan Diab, ya yi tir da kakkausar murya da abunda ya danganta da tsokanar soji mai hadarin gaske, biyo bayan jerin hare haren da tankokin yakin yahudawan mamaya na Isra’ila suka kaddamar a iyaka da kasar a jiya Litini.
Isra’ila dai na mai zargin kungiyar Hizbullah, da yunkurin kai mata farmaki batun da kungiyar ta musanta.
kungiyar ta Hizbullah ta sanar da cewa, makiya ne suka fara kaddamar da harin, kuma harbe-harben da aka yi ta ji daga bangaren makiya ne.
Bayanai daga yankin dai sun ce yanzu kura ta lafa bayan lamarin.
Isra'ila dai na cikin damuwa, ne tun bayan kisan data yi wa daya daga cikin dakarun kungiyar ta Hizbullah a baya bayan nan a kasar Syria.
SOURCE: ABNA24.COM
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Labaran Duniya