Ko Wanne Dan Uwa Wakilin Harka islamiyyah Ne!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BA DUK MAGANA TA WAKILIN HARKA KAN ZAMA MURYAR HARKA BA

Abubuwa biyu ne masu kama da juna amma ma'anarsu ta sha bamban . Wannan ya fassara su da ma'ana iri daya ya jahinci kalmomin.

A matsayinka na dan'uwa/dan shi'ah ya zama wajibi ka kasance mai yin taka-tsantsan cikin ayyukanka da zantukanka, domin kai fa wakilin harka islamiyyah ne a duk inda kake.

Duk wani abinda za kayi na addini ko mu'amala cikin jama'ah sukan fassara kane da aqidarka, wato duk abinda zai fito daga gare ka su kanga tamkar shine ma'ana ko muryar harkar, alhali sam ba haka bane.

Za ka iya aiki ko fururi wanda zai iya zama muryar harka, amma yawancin ayyukanka su zama muryar kanka ne ba na harka ba.

Saboda haka a matsayinka na wakilin harka islamiyya ka ji tsoron Allah tare da yiwa kanka adalci wajen yin wakilci na gari , domin munana ayyukanka da zantukanka zai iya zama cutar da harka da kuma jagoranta, uwa-uba kuma shine cutar da wanda ake yin harka din dominsa (A llah ).

Muryar harka kuwa ita ce abinda yake zuwa daidai da koyarwar jagora Sayyid Zakzaky (H ). Da yanzu wani zai fito yana magana ko ya aikata wani aiki wanda ya sabawa koyarwar jagora, to, wannan furuci ko aiki nasa ba zai zama muryar harka ba, ko da kuwa wannan mai magana ya sanya rawani da abaya .

MISALI:- Yanzu da ace za a sami dan Izala ko dan 'Dariqa ya aikata wani aiki wanda ya saba koyarwar tafiyar tasu, to, bisa adalci ba za ace wannan aiki nasa shine muryar tafiya ko karantarwarsu ba, zai zama aiki ne kawai na qashin kansa, amma yafi kyau ya kyautata komai nasa don zama wakili na gari.

A taqaice dai wannan shine bambanci tsakanin wakilce da murya.

Idan muka kalli yarjejeniyar yaqin Siffin zamu sami waraka, domin abinda Abu Musa Al-Ash'ari yayi wakilci ne, amma ba shine muryar Imam Ali (A.S )ba .

Tare da Ado Isah Guda.

           09039791509

ALAMIS, 9th July, 2020/ 18-11-1441. KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post