Karancin 'Yan Shi'a A Duniya, Miya Jawo Haka???


Tattare da cewa yan Shi'a kuna da Falsafa a magana, da iya kafa hujjoji, amma sai ga shi ku ne yan tsirari a cikin Musulmi, me ya janyo haka? Wannan ba alama ce ta cewa kuna kan bata da halaka ba ne?

Wasu daga cikin mutane suna yawan yin wannan maganar akan yan SHI'A saboda wasu sun Dan gamsu da hujjujinmu amma sai suki ganin sauran jama'a sunki bin wannan ta farki Allah sarki,
To, Abu na farko dai yana da kyau su gane cewa karanci da rashin yawa ba ma'auni ne na bata ko halaka ko rashin zama a kan daidai ko shiriya ba, asali ma Musulunci ya fi zargin yawa a kan karanci.

Mafi yawan yabon da Allah Ta'ala ke yi a Alkur'ani yana zuwa ne ga mutane yan kadan, kamar yadda mafi yawan zargin da Allah Ta'ala ke yi yana tafiya ne ga mutane masu yawa,
Misali: Allah Ta'ala yana yana cewa; Ba za ka samu mafi yawansu suna godiya ba, (A'arab 17). A wani wurin yana cewa; "A'a, mafi yawansu ba su yi imani ba. (Bakara, 100). A wani wurin yana cewa; " Kuma mafi yawansu fasikai ne. (Imran, 110, da Tauba 8). Awani wurin Allah ya kara da cewa "Kuma mafi yawansu ba su da hankali. ( Ma'ida, 103). A wani wuri yana cewa: Sai dai mafi yawansu jahilai ne. (An'am, 37, da An'am 111). Awani wurin yana cewa kuma mun samu mafi yawansu fasikai ne.(A'araf 102). A wani wuri yana cewa; " Idan ka bi mafi yawan mutanen da ke kasa, za su batar da kai daga ta farkin Allah. (An'am, 116).

Ayoyin da suka zargi yawa suna nan rututu a cikin Alkur'ani. amma bara na barsu haka
Sannan a gefe guda wasu ayoyin na Alkur'ani sun yi ta yabon mutane yan kadan, misali, Allah Ta'ala yana cewa "Sau da yawa jama'a kadan sukan rinjayi jama'a masu yawa da izinin Allah.(Bakara). Awani wurin yana cewa Kuma mutane kadan ne daga cikin bayinmu suke godiya. (Saba'i 13). A wani wuri yana cewa, " Kadan ne masu hankalta. A wani wuri yana cewa, Masoyansa kawai sune masu takawa, sai dai mafi yawansu ba su sani ba.(Anfal,34).

Wandan jerin ayoyi sun tabbatar mana cewa, yawan mabiya ba shi ne ma'aunin zama a kan daidai ba, kuma karanci ba shi ne ma'aunin bata ko halaka ba, hasalima yawan ya fi nuna alamar halaka a mafi yawan lokuta.
In yawa shi ne ma'aunin zamowa a kan shiriya, to sai mu ce; Tabbac Ahluls_sunna sun fi yan Shi'a yawa a duniya.

Amma kiristoci da yahudawa da marasa addini sun ninka Ahlus-sunnah yawa a duniya kunga da sai a ce sune akan gaskiya kinan?
Imama Ali yana cewa Kasan gaskiya ta hanyar sanin ma'abutanta, Kuma ka San karya ta hayar sanin mutanenta.
In kana so ka gane Shi'a shiriya ce ko halaka, kar ka kalli karancinsu, ka duba ka gani, shin yan Shi'a su waye su a duniyar Musulunci? Wace gudummawa suka bayar wajen gina ci gaban Musulunce?

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post