Jarabawa Ce Ko Wanne Ana Nan Ana Jarabta Shi – Sheikh Zakzaky (H)





Naqaltowa: Bin Haroun Sigau

Ka ga waɗannan jarabawowin suna nan har yanzu Allah Ta’ala yana jarraba mu da jarabawowi, ya ga cewa ko kai ahalin wannan ne? Dubi inda Allah Ta’ala yake tarbiyyar Manzonsa a cikin surar ‘Muzzamil’. Yana cewa “Inna Sa Nulqee Alaika Qaulan Saqeela”. Bayan da ya ce masa ya tsaya da sallar dare. “Qumillaila illa Qaleelah, Nisfahu Auwinqus Minhu Qaleela, Auzid Alaihi Warattilil Qur'ana Tarteela, Inna Sanulqee Alaika Qaulan Saqeela”.

Za mu jefa maka zance mai nauyi. Masu fassara sun ce ma'anarsa shi ne aiki da abin da aka umurce ka ko aka hana. Wato kai ne za ka zama kyakkyawan siffa na duk abin da aka ce a yi. Alhamdulillahi kuma haka Manzon nan ya kasance. Duk abin da Alqur'ani ya ce a yi, shi ne mafi kyawun misali na aikata wannan abin. Wato kenan jarrabawa ce wanda kuma kowannenmu ana nan ana jarabta shi. Za a jarabta ka da kayan kwadayi. Kun san jarabawa yadda ake yi? Da ana yin jarrabawa yadda yake ba za ka iya ci ba, to da bai zama
jarrabawa ba. Da kuma za a yi jarabawar da kowa ma zai ci, ba wanda ba zai ci ba. Kamar a ce in kana jin yunwa ka ci abinci. Wanene ba zai ci wannan jarrabawar ba? Ai ba jarrabawa ba kenan ko? Jarrabawa ita ce, kana jin yunwa kada ka ci, to jarrabawa kenan.

Ko kuma kana jin qishi kar ka sha ruwa. Kamar wadanda aka jarabta su din nan, jama'ar Dalut (AS), wanda kafin su je su kara da jama'ar Jalutu jabberi. Bayan sun shawo rana, sun yi tafiya sun shawo rana, sai aka ce ga su nan za su gangara gulbi akwai ruwa, amma kada a sha. In kuma an haye gulbin za a hadu da maqiya za a fafata yaqi. Amma in an gangara aka kalli ruwan, a kalla kawai a wuce. Amma in ka kasa daurewa, ka ga ba za ka iya ba, to ka kamfata sau daya, shi kenan ka wuce, kar ka yi kamfata biyu da hannuka. Sai wasu suka ce "a'a, to in mun haye ba za mu yi karo da maqiya ba ne?" A ka ce Eh. "To! Ba in muka sha ruwa ba sai mu sami qarfin yaqi? Aka ce, to ai Allah ne ya ce kar a sha ruwan.

To ka ga “Innallah Mubtaleekum bi Nahar, Faman Shariba Minhu fa Laisa Minnee, Wamanlam Yad'amhu fa Innahu Minnee illa Manigtarafa Gurfatan bi Yadih”. Sai dai wanda ya yi kamfata daya rak, to shi yana tare da wannan Manzo. Ka ga wannan ba qaramar jarabawa bace. Ka kwaso qishi, ka ga ruwa a ce kar ka sha. Amma ka ga wasu sun ci jarabawar, kadan ne kuwa suka ci wannan jarabawar. Sai wasu suka wuce suka yi dauriya na sosai.

Su ka ce tunda yake dai an ce kar mu sha, ba za mu sha ba. Sai wasu suka ce ai an ce ka kamfata daya, suka dan kamfaci daya din suka wuce. Mafi yawa suka kwankwada. Da suka haye, sai wadanda suka kwankwadi ruwan nan suka hango Jaluta da jama'arsa, suka ce,
"a'a, a'a, “La Dakata Lanal Yauma bi Jaluta wa Junudihi." Sai suka jiyo baya, suka ce wannan ai ba yaqi bane, kashe mu kawai za su yi.
Su kuwa wadannan wadanda ba su sha ruwan ba, da wadanda suka yi kamfata daya suka ce; “Kam min Fi'atin Qalilatin Ghalabat Fi'atan Kasiratan bi Izinillah, Wallahu Ma'assabireen”. Sai suka yi nasara a kansu suka rinjaye su da izinin Allah. Ya zama yaqin ma dai Allah ya yi
masu.

Cikin Jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky a wajen rufe taron qarawa juna sani na yini uku (Mu'utamar), a garin Talatan Mafara jihar Zamfara a 2008.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post