Kakakin ma’aikatar kiwon lafiya a nan kasar Iran ta bayyana cewa an gano mutane fiye da 2000 wadanda suka kamu da cutar Corona a jiya Lahadi sannan adadin wadanda suka warke daga cutar ya kai kimani dubu 220.
Majiyar muryar JMI ta nakalto Simo Saadaat Lari tana fadar haka a jiya Lahadi. Ta kuma kara da cewa mutane 2186 suka kamu da cutar a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata a yayinda 1499 suke jinya a cikin asbitoci a kasar.
Lari ta kammala da cewa ya zuwa yanzu mutane dubu 257,303 suka kamu da cutar a duk fadin kasar, sannan muatne 194 suka rasa rayukansi a jiya kadai, wanda ya sanya adadin wadanda suka rasa rayukansu saboda cutar ya kai mutane 12,829. Sai kuma 219,993 ne suka warke daga cutar.
Wadanda suka kamu da cutar a duniya ya kai mutane miliyon 12,865,000 a yayinda dubu kimani 569 daga cikinsu suka rasa rayukansu. Aci gaba tare da rubu’in wadanda suka kamu da cutar.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Labaran Duniya