Iran Ta Nuna Rashin Amincewarta Da Kudurin Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Kan Siriya



HOTO DAGA ABNA24.COM SOURCE: ABNA24.COM


Wakilin kasar Iran a hukumar yaki da makamai masu guba ta duniya wacce take da mazauni a kasar Holand ya bayyana matsayin da hukumar ta dauka kan kasar Siriya a matsayin wanda babu adalci a cikinsa, sannan da alamun an shigarda siyasa cikin lamarin.

Ali Riza Kazimi andi , wakilin kasar Iran a hukumar ta yaki da makaman guga ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce hukumar ta kammala taron ta na 94 inda a karshen zaman ta amince da wani kuduri wanda yake tabbatar da cewa gwamnatin kasar Siriya ta mallaki makaman guba kuma ta yi amfani da su kan mutanen kasar.

Wakilan kasashe 29 ne suka amince da kudurin, a yayinda wakilai 9 suka kauracewa zaben sai kuma 3 wadanda suka nuna rashin amincewarsu, kuma su ne Iran, Rasha da kuma China.

Abin mamaki shi ne kasashen turai wadanda suka sayarwa Sadam Husain na kasar Iraqi makamai guba wadanda ya yi amfani da su kan mutanen Iran da kuma mutanen kasar ta Iraqi a shekara 1980 suna daga cikin kasashen da suke tuhumar kasar Siriya da wannan zargin, wanda bai da tushe balle makama.

Har’ila yau kasashen Iran da Rasha da kuma wasu kasashe 17 sun fidda bayani bayan wannan taron inda suke tabbatar da cewa wannan kudurin da hukumar ta fitar kan kasar Siriya karayce a fili, kuma hukumar suna son amfani da shi ne don taimakwa kasashen yamma wajen cin mutuncin gwamnatin kasar ta Siriya nan gaba.

SOURCE: (ABNA24.com)

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.maasumah.com.ng/


IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :


 MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post