Inda Mu Masu Kisan Kai Ne, Masu Kashe Wani Ne, Da Mun Kashe Wadanda Suka Bude Mana Wuta Rana Tsaka – Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)



INDA MU MASU KISAN KAI NE!!!

To inda mu masu kisan kai ne masu kashe wani ne da, mun kashe wadanda suka bude mana wuta rana tsaka. Amma akan ganmu har muna hannu dasu. Wanda suka bada umarni suka bude wuta akan mu rana tsaka mun san su, sun san mun sani, amma har su kan miko hannu mu gaisa. Amma iya kan sanin mu Albani har suka kashe shi bai taba kashe kazar mu ba, ko ya fasa kwan mu. Ko kuna da labarin ya taba kashe mana kaza?

 To ga wanda suka bude mana wuta rana tsaka mun san su, wa muka kashe a cikin su? To ballantana ma ko su magidantan su na waje Amerika da Isra'ila duk kirkiro kungiyoyin ta'addanci da suke yi suna cewa kungiya kaza na musulmi, basu iya kirkiro kungiyar Shi'a na ta'addanci ba, bai yiwu musu ba, sun iya kirkiro na ama ne (Wanda ba 'yan Shi'a ba) saboda su ama kara zube suke basu da shugaba, kowa shugaban kan sa ne.

 Su ko Shi'a hatta ka mari mutum baza ka iya ba sai da izinin Mushtahidi. Mushtahidi yana nufin Ayatullah, Shi'a ba yana daukan abin da yaga dama bane, komai zai yi dole ya zama bisa ka'ida ne. Saboda haka horo wanda za a ji zafi ittifakan ka tambaya, ba ayi sai da izinin Mushtahidi, ballantana kisa, horo wanda za a ji zafi koda duka ne mutum ba zai yi ba sai da izinin Mushtahidi. Wannan a duk duniyar Shi'a haka yake ba sabani, ba ra'ayi na biyu. Sannan yaqi iftida'a aje a samu wadansu mutane a yake su da unwanin ana yakar su da su shiga muslunci ba wanda ke da izinin bada wannan sai Imam Mahadi (AF) ya bayyana, wannan ittifaqan duk kaje duniyar Shi'a gaba daya kowane abin da zai gaya maka kenan.

 Saboda haka babu yanda za ayi kaji wani yaje ya kai hari da unwanin Jahadi yaje ya kai hari indai Shi'iii ne ba a taba ji ba. Don haka ma su masu kirkiro kungiyoyin ta'adda su jinginawa musulmi America da Isra'ila basu taba kirkiro kungiyar Shi'a ba suka kai wani hari, na Ama suke yi. Don haka ma sai kaji sun ce Sunnah kaza basu taba kirkiro na Shi'a ba, saboda sun san ba wanda zai yarda, saboda ba yanda za ayi Shi'ii ya kai ma wani hari. Domin shi yasan cewa indai yaki ne da unwanin yaki sai Imam Mahadi ya bayyana, amma da unwanin kariya shine ya zama wajibi in an kai maka hari ka kare kan ka, amma bada unwanin Kai ka Kai hari ba, sai Imam Mahadi ya bayyana. Saboda haka wannan zai zama wauta bayan kun yi ta'addancin Ku kuzo kuce zaku jinginama wani, wannan shi ake cewa "Baudani".

 Bayan ku kuyi wannan aika-aikar kuma wai kuna neman zaku qalama wani. Kuma ku rasa wanda zaku qalama sai wanda ba yanda za ayi wani ya yarda duk duniya. Ko a yanzu kana zaune kaji ance wasu Shi'a a khashmir sun kai hari kasan karya ne.

 - Sheikh Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky (H) a cikin jawabin sa lokacin yunkurin alakanta Shi'a da kisan Sheikh Albani.
 Naqaltowa: Ibrahim Almustapha Saminaka KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post