Idan Har Mijinki Zai Barki Kiyi Karatu, To Lallai Wannan Mijin Naki Ba Abin Wulakanta Bane


Dayawan lokuta nakan nunawa yan uwa na maza muhimmanci barin matansu su cigaba da karatu, ko ba komai Sabo da yanayin hali da muka tsinci kanmu aciki, a wannan kasa, domin yanxu lokacine na ilimi, duk wata kasar da zaka nunata da yatsa zakaga da ilimi take tinkaho musamman ga masu tasowa, basa da wasa a fagen ilimi Sabo da sunsa muhimmanci sa, ba kamar wannan kasa da muke zaune ba, bakasan ma ina aka dosaba kullum cikin baganniya kamar shanu marasa makiyayi.

Shakka babu ilimi ga ya mace yana dagayar muhimmanci, domin idan har kanaso kalalata ko wacce kasa ce, to matakin farko lalata matan kasar ma'ana sukasance an wargaza tarbiyansu, to daganan kasa tafara lalacewa, domin sune tarbiya take hannunsu. To, yanxu sai mukazo zamanin da ko ta wanne fanni ya kamar mu akeyi, mutum yasani ko bansaniba, amman idan lokaci yayi zai fahimci haka. Ta yadda da ilimine zamu iya fuskantar ko wanne kalubale a rayiwar mu, da shi zamu iya yakar zalinci dake wannan kasa, Sabo da haka wajibi mubar matan mu su nemi ilimi, ko ta wacce fuska, yanzu ba lokacine na jinkida da kallan raye Raye ba, a lokacine na fafutukar samarwa da kasar mu yanci, da hanbar da zalinci ta hanyar ilimi da kuma hikima.

Soba da haka wasu kecewa da ni, shakka babu barin mace ta cigaba da karatu abune muhimmi ko ba komai domin yaran ka su taso dasanin muhimmanci ilimi, baya gahaka zaka bakasan ya rayiwa zata kaya ba, su kace dani matsalar shine kabawar mace taje tayi karatu na zamani karshe tazo ta rainaka tanuna kai jahiline bakasan komai ba, gwara abarsu acikin duhun jahilcinsu sai yadda kai dasu, ko raini ya shiga tsakaninku, shiyasa da yawa maza suke tsoran auran yar boko, Sabo da yanayin rayiwa zata nunama ka, kai bakasan komaiba.

Nace da su hakane da yawan maza bansan adadiba suna cewa haka, kuma na yarda amman ga mace me tunanini ga duk namijin da zai barta ta cigaba da karatu to wannan ba abin rainawabane, wajibi kiyi masa biyayya, domin da yawa mata suna San cigaba da karatu amman maza jansune basa barinsu, wasu kuma mazan na burin suga matansu sun cigaba da karatu amman suna jin me zaije yazo.

To, mu dai abin da ya kamata maza shine muyi Abu domin Allah mubar matanmu sunemi ilimi su cigaba da karatu, kaidai kasauke hakkikin da ke kanka, ruwan ta tayi biyayya gareka ruwan ta ta kiyi amman kai kasauke hakkin da ke kanka. Amman tasan baka zalincetaba.

Kirana ga sauran matan da suka cigaba da karatu, ma'ana maza jansu suka barsu suka cigaba da karatu, a matakin gaba da secondary shine, kuzamo kamammu domin domin wasu zakaga kamewar su da sauki, watama sai kayi zatan budurwace amman zaka tarar wai matar aure ce, Sabo da haka ya kamata kurinka kulawa hatta a mata kusan dawa zakuyi mu amala.

Wassalamu.....kum

©Habibu R Nasrallah

Email: Habibrabiu81@gmail.com

Share to others👆

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post