Hotuna: Dalibai Yan Academic Forum Na Jihar Zamfara, Sun Ziyarci Da'irorin T/Mafara Da Maradun



A ranar Assabar ta makon da ya gabata 11/07/2020 ne; 'Yan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky [H], masu karatu a makarantun gaba da Sakandare, suka gudanar da ziyarar gabatar da kai ga wakilin 'yan uwa na Da'irar T/Mafara, Malam Abubakar Nuhu (Malam Abba), da na Da'irar Maradun, wato Malam Saleh Salisu Maradun.

Ziyarar wadda daliban suka gabatar da nufin bayyanawa wakilan 'yan uwan kudurinsu na farfado da ayyukan wannan dandali a fadin jihar, da kuma neman sa albarka daga wurinsu, ta samu babban tarbo daga duka wakilan 'Yan uwan na wa'ennan Da'irori guda biyu. Kuma sun yi marhaban tare da nuna jin dadinsu akan wannan yunkuri da wa'ennan daliban suke kokarin yi.

Da yake gabatar da jawabi ga wa'ennan dalibai a muhallin Makarantar Fodiyya Islamiyya da ke Maradun, Malam Saleh Salis Maradun, ya bayyanawa daliban cewa; lallai wannan jiha ta Zamfara tana daga cikin jihohin da su Sheikh Zakzaky [H] suka damu dasu ta fuskoki daban-daban; “Ina tabbatar muku cewa, lallai inda Malam [H], zai ji labarin wannan yunkuri naku, to babu shakka zaiyi matukar jin dadi, saboda, su Malam suna matukar son yunkurin 'yan uwa na wannan jiha”.

Ya kara da cewa; “Nasan a shekarun baya (2012), Sayyed [H] da kansa ne yace; a Gusau za a yi Mu'utamar na Academic Forum na kasa gaba daya, saboda son da yake yiwa wannan jiha” In ji Malam Salis Maradun.

Haka shima Malam Abubakar Nuhu (Malan Abba) Wakilin 'yan uwa na Da'irar T/Mafara, a lokacin da yake kar6ar bakuncin wa'ennan dalibai a gidansa dake Mafara, ya nuna musu muhimmancin ayyukan wannan Forum da suke so su farfado da shi, kuma ya basu shawarwari na zamantakewar yau da kullun, don inganta ayyukan wannan forum; “Ku sani cewa wannan aiki da kuka dauko ba karamin aiki bane, don haka sai kun rika yin abu da Ikhlasi. Ku gujewa jin kyashin wani, kuma duk abunda zaku yi, to kada ku kaucewa hadafin wannan harka. Duk wanda yazo muku da abunda ya sa6awa hadafin wannan harka, to ku barsa da kayansa, ku tsayu akan abunda Malam [H] yake kira”

Malam ya cigaba da cewa; “Kuma a dage sosai wajen yin Sana'o'in hannu, ko kasuwanci, kada a dogara da albashi, ko Noma ne ya kamata mutum yayi, domin albashin wannan kasa tamu ba zai iya wadatar da ma'aikata ba. Duk Wanda ya dogara da albashin Najeriya, to sunanshi bashi. Nima nan da kuke ganina, ban zauna haka nan ba, nasan a cikinku da wasu zasu ganni cikin gona, kila bazasu ganeni ba.” Inji Malam Abba Mafara.

Daga karshe, mai magana da yawun daliban, ya bayyana cewa; sunada kudurin gabatar da irin wannan ziyara ga duka wakilan 'yan uwa na Da'irorin da suke jihar Zamafara, don haka wannan ziyara zata cigaba Insha-Allahu.

®Sharief Munauwar Mukhtar.

Ga hotunan da muka dauko👇



KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post