~Aljawadu Shi'a Kagara
Tabbas Yanzu ne Loqacinda Ya Kamata duk Wani Dan jarida [Media] na Harka Ya Bawa Harka Gudunmuwa Ta Hanyar Isar da Saqon Harka Da Kuma Bayyanawa Duniya Irin Zaluncin Da Akeyiwa Malam Ibraheem El-Zakzaky (H) da mai Dakinsa Malama Zeenat da Sauran Amajiransa.
Tun Bayan Dawowar Su Sayyeed Daga kasar India Bamu Qara Ganin Video,Audio Na Maganar Malam Zakzaky (H), Azzalumai Sunyi Shiru Akan Batun Malam Zakzaky (h) kwata-kwata Basa magana akan su malam duk da daman munsan koda yaushe shirinsu Shine ganin bayansu Sayyeed Basu da Niyyar Sakinsu.
'Yan uwa muma mun gajiya da batun su Sayyeed, To yanzu mu 'Yan Media muya kamata Mu tashi domin Nunawa Duniya Irin Zaluncin da Akeyiwa Su Malam Zakzaky (H) kada Zancen Covid-19 tasa muqi Yada Zaluncin da Akeyiwa Jagoran mu, Tabbas da Zamu Duqufa Wajen Isar da Mazalumiyyar Jagora Na Tabbata Zamuga Natijar Hakan.
Mu Tursasa Masu Da Bayyana Zaluncinsu Ga Duniya Harsu Sakar mana Jagoran mu.
#FreeZakzaky[h]✌🏻
#313Battalion✌🏻
Tags:
#FREE_ZAKZAKY