Hadisai Arba'in Daga Bakin Imam Ali Al-ridha (A.S)


'ma'asuma Nigeria news update,

-Imam Rida[AS] ya ce, “Duk wanda Allah Ta’ala yayi ma ni’ima to wajibine ya yelwata ma iyalinsa.”

 2-Imam Rida[AS] ya ce, “Lokacin da bawa ya fi kusanci ga Allah Ta’ala shine lokacin da yake cikin sujuda.”

 3-Imam Rida[AS] ya ce, “Mai kyauta yana kusa da Allah,yana kusa da Aljanna,yana kusa da mutane,yana kuma nesa daga wuta.”

  4-Imam Rida[AS] ya ce, “Marowaci yana nesa da Aljanna,yana nesa da mutane,yana kuma kusa da Wuta.”

5-Imam Rida[AS] ya ce, “Kyauta wata itaciya ce cikin Aljanna rassanta na cikin Duniya,to duk wanda yayi riko da wani reshe daga cikin rassanta to zai shiga Aljanna.”

 6-Imam Rida[AS] ya ce, “Duk wanda ya yi ma kansa hisabi to zai rabauta,wanda kuma ya gafala da yi ma kansa hisabi to zai yi hasara.”

 7-Imam Rida[AS] ya ce, “Mafificiyar dukiya itace wadda mutum ya kiyaye mutuncinsa da ita.”

  8-Imam Rida[AS] ya ce, “Mumini ko da ya fusata to fusatarsa ba zata sa ya yi abinda ya saɓa ma shari’a ba.”

9-Imam Rida ya ce, “Bawa ba zai samu hakikanin kamalar imani ba har sai ya siffata da abu ukku:Ilimi a fagen addini.Tsaka-tsaki a fagen rayuwa.Dauriya akan jarabawowi na musibu.”

10-Imam Rida ya ce, :Imani yana da ginshikai guda huɗu sune:Dogara ga Allah,yadda da hukuncin Allah,sallamawa ga al’amarin Allah da kuma fawwala al’amura zuwa ga Allah.”

11-Imam Rida ya ce, “Duk wanda bai gode ma Mutane kan wani abin alhairi da aka yi masa ba to ko ba zai gode ma Allah ba.”

 12-Imam Rida ya ce, “Musulmi shine wanda sauran Musulmi suka kuɓuta daga harshensa da kuma hannunsa.” Wato baya cutar da ‘yan uwansa Musulmi da harshensa misali yi masu giba ko Annamimanci da dai sauransu.”

 13-Imam Rida ya ce, “Ka kyautata zato ga Allah Ta’ala saboda duk wanda ya kyautata zato ga Allah to Allah yana nan a yadda yake zatonsa.”

14-Imam Rida ya ce, “Taimaka ma raunanna yana daga cikin mafificiyar sadaka.”

 15-Imam Rida ya ce, “Yana daga cikin Sunnar Manzon Allah yin walima lokacin Aure.”

 16-Imam Rida ya ce, “Ibada ba itace yawan sallah da azumi ba,amma ibada itace yawan tafakkuri-tunani- ga al’amarin Allah Ta’ala.”

17-Imam Rida ya ce, “Marowaci bai da hutu,mai hassada kuma bai da jindaɗi,maƙaryaci kuma bai da mutunci.”

18-Imam Rida ya ce, “Allah Ta’ala yayi umrni da Sallah da kuma ba da Zakka to wanda yayi sallah amma bai ba da zakka ba to ba za a kar~i sallar shi ba.”

  19-Imam Rida ya ce, “Mumini shine wanda idan ya aikata mummuna to ya kan yi istigfari.”

 20-Imam Rida ya ce, “Duk wanda ya kwatanta Allah Ta’ala da halittarsa to yayi shirka,duk kuma wanda ya jingina masa abunda aka hana a jingina masa to ya kafirta.”

 21-Imam Rida ya ce, “Yana daga cikin alamomin Fa}ihi ha}uri,ilimi da kuma yawan shiru.”

 22-Imam Rida ya ce, “Allah Ta’ala baya son yawan roko da kuma tozarta dukiya.”

23-Imam Rida ya ce, “Kowane Mumini Musulmi ne amma ba kowane Musulmi yake Mumini ba.”

 24-Imam Rida ya ce, “Yana daga cikin ]abi’oin Annabawa yin tsafta da kuma sa turare.”

 25-Imam Rida ya ce, “Ka sadar da zumunci ko da ko da kur~in ruwan sha ne,mafificin abinda zaka sadar da zumunci dashi shine kamewa daga cutarwa.”

26-Imam Rida ya ce, “Duk wanda yayi biyayya ga Allah Ta’ala to za a yi masa biyayya.”                                                                                 

 27-Imam Rida ya ce, “Duk wanda ya ji tsoron Allah Ta’ala to za a ji tsoron sa.

28-Imam Rida ya ce, “Sallah a farkon lokaci yafi falala,kuma ka da ka yi sallah a bayan fajiri.”

 29-Imam Rida ya ce, “Mai sata ba zai yi sata ba lokacin da yake satar yana da imani.Mai shan giya ba zai sha giya ba lokacin da yake shan giyar yana da imani.Mai kisa ba zai yi kisa ba ba tare da ha}}i ba lokacin da yake kisan yana da imani.”

 30-Imam Rida ya ce, “Imani shine }udurtawa da zuciya,furuci da harshe da kuma aiki da ga~o~i.”

 31-Imam Rida ya ce, “Manzon Allah[S] ya ce, “Duk wanda ya ganni a cikin barcinsa-mafarki-to ha}i}a ya ganni domin Shai]an bai iya siffata cikin siffata.”

32-Imam Rida ya ce, “Babu wani Mumini da zai ziyarce ni fa ce Allah ma]aukaki ya haramta jikinsa daga wuta.”

33-Imam Rida ya ce, “Za a kashe ni ta hanyar sa mani guba,kuma kabari na zai kasance wajen kai komo na shi’ata, to duk wanda ya ziyarce ni to zan ziyarce ranar kiyama.”

34-Imam Rida ya ce, “Duk wanda ya ziyarci kabarina to Allah Ta’ala zai rubuta masa ladar shahidi dubu ]ari kuma za a ta da shi a cikinmu.”

 35-Imam Rida ya ce, “Wallahi babu wani daga cikinmu-Aimma- face an kashe shi domin ya kasance shahidi.”

 36-Imam Rida ya ce, “Duk wanda ya yarda da ka]an na arziki da Allah ya bashi to Allah zai yarda da aikinsa ka]an da ya gabatar.”

 37-Imam Rida ya ce, “Wani zamani zai zo ma mutane zaman lafiya in ka kasa shi kashi goma a lokacin to kashi tara yana ga nisantar mutane,kashi guda kuma ga yin shiru.”

 38-Imam Rida[AS] ya ce,Imam Ali[AS] ya ce, “Bai halatta ga wani Musulmi ba ya tsorata ]an uwansa Musulmi.”

39-Imam Rida[AS] ya ce Manzon Allah[S] ya ce, “Duk wanda ya kame fushinsa to Allah Ta’ala zai kame daga yi masa azaba.”

 -40-Imam Rida[AS] ya ce,Manzon Allah[S] ya ce, “Duk wanda ya kyautata halayensa to Allah Ta’ala zai kai shi ga matsayin mai yawan sallah da azumi,

Amincin allah Yatabbata ga limaman shariya ya barmu a naku tafarkin,

Allah T yakubutar mana da Jagora gaskiya daga hannun azzalumai nijahee Sayyadina rasulullah,
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post