GWAMNATOCI KUNCE AYI NOMA AMMA KUN KI BADA TAKI.



Wani abu sai kasata najeriya, inda zakaga kare na tallar tsire, kaza nawa zakara Barbara, kaga saniya na tatsar nonon bafulatana, kare ya koro kura, kaga doki akan mutum, Wadannan abubuwane Wanda basu yiwuwa a zahiri, duk da ikon Allah yafi da haka, amma shugabannin najeriya sai suce sunji Sun gani zasu iya aikata haka.

Tun da gwamnatin nan ta shigo take cewa a inganta noma, domin a samawa kasa abinci tare da samun aikinyi, amma abin takaici sai ka rasa ta yadda noman zai inganta alhali babu tsari na gaskiya sai coge, karya ha'inci da babakere daga bangaren gwamnati, jami'anta da kuma wasu masu da'awar shugabantar kungiyoyin manoma. Suma yan kasar ba'a barsu ba, wani lokacin har da yan kasashen makwafta ake iya shegen.

Duk wani abu dazai tallafawa noma an kashe shi a kasar nan baya aiki, ma'aikatan gona a takarda kawai suke aiki, dan abin daya rage shine taki da ake badawa, to shima gaya nan yana neman gagara, koda za'a bada shi da tsada ake badawa, kuma wani abin takaicin idan an tashi dabawa sai a bada kurarren lokaci, damina tayi nisan gaske, Amma a haka kullum ake cewa ayi noma! Ko damai za'ayi noman?

Yanzu haka an shiga wata na biyu da faduwar damana a nan arewacin najeriya, wasu manoman har Sun fara maimai (noma na biyu) amma har yanzu babu taki ba labarinsa, wani abin haushin ma wai sai yanzu wasu jahohin ke shirin kaddamar da bada kayan noma na bana. amma a haka ake cewa ayi noma.

Kuma Idan kace Zakasayi taki a kasuwa sai ka dora akan kudi dubu goma duk buhu, ya ilahi talakka Wanda yake fama da sayen gero, dawa ina yaga wannan kudi da zai sayi taki? Amma wai a haka ake cewa ayi noma.

Wani abin bakin cikin shine tallafin da ake badawa na noma an samu bata gari marar sa kishin kasa maciya amana masu ci da gumin talakka wai sune shugabanni wannan harka, wani Dan Iskan baima san hanyar gona ba, wani kuma ya dauki manoma yan wahala, amma wai sune shugabanni rabon tallafin noma, kuma gwamnati na kallo ta kyale, wai a haka ake Cewa ayi noma.

Ina kira ga wannan gwamnati ta buhari idan har da gaske take akan harkar noma ta dawo ta sake tunani tare da tuntubar manoma na kirki tun daga rumfar Zabe har zuwa karamar hukuma, jaha ta haka ne za'a rabe aya da tsakkuwa akuma samu sakamako Mai inganci.

Idan kuma har kunsan bazaku gyara tsari ba, Don Allah ku rabu damu da karyar banza ku kyale mu kawai muyi noman mu na gado da muka saba da takin shanu, awaki da toka.

Musa Ibrahim Daura.
15-7-2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post