Falalar Yan Uwantaka tsakanin Musulmi



'Ma'asuma Nigeria nigeria,

Bismillahi rahmanir Rahim

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da daukaka, wanda sanya muminai yan uwan juna, sashinsu na taimakon sashi. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa, har zuwa ranar sakamako,

Lalle ne yan uwantaka tsakanin mutane a addini bai takaita ga musulmai kadai ba, har ga wadanda ba musulmai ba sukan zama yan uwa a addininsu, amma yan uwantaka ta musulunci ya fi kowani irin yan uwantaka, saboda shi yan uwantaka ne akan addinin gaskiya, kuma alakar bata yankewa har bayan mutuwa. Allah Madaukakin sarki yace: "Masoya a wannan yinin abokan gaban juna ne, face masu takawa". Suratuz Zukhruf: 67.

Hakika Allah Ya sanya yan uwantaka ta Musulunci ta fi yan uwantaka ta jini, kuma ya shar'anta son junan su da kuma yin duk abinda zai karfafa yan uwantaka a tsakanin su, saboda da hakan ne addini zai tsayu, kuma a samu taimakekeniya a tsakanin musulmai.

Haka kuma Allah Ya hana duk wani abinda zai bata yan uwantaka, zai kawo sabani a tsakanin musulmai. Allah Yace: "Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku a lokacin da kuka kasance makiya, sai Ya sanya soyayya a tsakaninku, saboda haka kuka wayi gari da ni'imarSa yan uwa. Kuma kun kasance a kan gabar rami na wuta, sai Ya tsamar da ku daga gare ta. Kamar haka Allah Yake bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku za ku samu shiryuwa". Suratu Al 'Imran: 103.

Yan uwantakan Musulunci bata tsaya lokacin zaman lafiya tsakanin musulmai ba, har ma lokacin fada da juna suna nan a matsayin yan uwan juna, kamar yadda Allah Yace: "Kuma idan jama'a biyu ta muminai suka yi yaki, to ku yi sulhu a tsakaninsu," har zuwa inda Allah Yace: "Abin sani kawai muminai yan uwan juna ne, saboda haka ku yi sulhu a tsakanin yan uwanku biyu". Suratul Hujurat: 9-10

Musulunci ya wajabtawa musulmai idan sun hadu da junansu su yiwa junan su sallama. Saboda sallama tana karfafa imani, wanda shine sababin shiga aljanna. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: "Wallahi ba zaku shiga aljanna ba har sai kun yi imani. Kuma ba zaku yi imani ba har sai kun so junan ku. Shin baku so in nuna muku abinda in kuka yi shi zaku so junan ku? Ku yada sallama a tsakaninku". Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Kuma Muslunci ya hana musulmi ya kauracewa dan uwansa musulmi, saboda hakan zai haifar da kiyayya da gaba a tsakanin su, sai in ya zama kauracewar saboda yana aikata wani sabo ne.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: "Musulmi dan uwa musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya mika shi ga halaka, duk wanda ya biyawa dan uwansa bukatunsa, to Allah zai biya masa bukatunsa. Duk wanda ya yaye wa musulmi bakin ciki, to Allah zai yaye masa bakin cikin ranar al-kiyama. Duk wanda ya suturce wani musulmi, to Allah zai suturce shi rananr al-kiyama". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: "Kada ku yi fushi da junan ku, kuma kada ku yiwa junan ku hasada, kuma kada ku juyawa junan ku baya, kuma ku kasance bayin Allah yan uwan juna. Kuma baya halatta ga musulmi ya kauracewa dan uwansa sama da kwana uku". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Haka nan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: "Ana bijiro da ayyuka (ga Allah) a duk ranar alhamis da litinin, sai Allah Ya gafarta a wannan ranar duk mutumin da baya shirka, sai mutumin da ya kasance akwai gaba a tsakanin shi da dan uwan shi, sai a ce: Ku jinkirtawa wadannan har sai sun yi sulhu, ku jinkirtawa wadannan har sai sun yi sulhu". Muslim ne ya rawaito shi.

Saboda haka Musulunci ya haramta musulmi ya kauracewa dan uwansa fiye da kwanaki uku kamar yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya fada: "Bai halatta musulmi ya kauracewa dan uwan sa ba fiye da kwana uku, su hadu da juna, wannan ya juya baya, wannan ma ya juya baya, kuma mafi alherinsu shine wanda ya fara yin sallama". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Falalar yan uwantakan Musulunci

Yan uwantakan musulunci yana da falala mai yawa. Ga kadan daga cikin su:

Yan uwa masu son junan su saboda Allah zasu kasance karkashin al'arshin Allah ranar kiyama. Saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: "Mutum bakwai zasu kasance a karkashin inuwar Allah, ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa". Sai ya ambaci cikinsu: "Da mutum biyu wadanda suka so junan su don Allah, suka hadu a kan sa, suka rabu akan sa". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Allah Madaukakin Sarki yana son masu son junan su saboda Allah. Kamar yadda ya zo a kissar mutmin da ya ziyarci dan uwansa a wani kauye saboda yana son shi don Allah, sai mala'ika ya sanar da shi cewa; "lalle Allah Yana son shi". Muslim ne ya rawaito hadisin. Haka nan Allah yace a cikin hadisul kudusi: 'soyayyata ta wajaba ga masu son junan su saboda ni".
Duk wanda ya so dan uwansa saboda Allah, to zai dandani zakin imani. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: "Abubuwa uku duk wanda ya samu kansa a cikin su, to ya dandani zakin imani; Ya zama Allah da ManzonSa sun fi soyuwa a gare shi fiye da wanin su. Kuma ya so mutum domin Allah ba don komai ba, sai don Allah. Kuma ya kyamaci komawa kafurci bayan Allah ya tsamar da shi daga kafurci, kamar yadda yake kyamatar a jefa shi wuta".
Soyayyar juna don Allah yana tabbatar da imani, kuma yana zama sababin shiga Aljannah. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: "Ba zaku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani. Kuma ba zaku yi imani ba har sai kun so junanku. Shin baku so in nuna muku abinda in kuka yi shi zaku so junan ku? Ku yada sallama a tsakaninku". Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Abubuwan da suke jawo soyayyar juna, kuma su karfafa yan uwantaka a Musulunci

Musulunci ya shar'anta abubuwan da zasu hada kan musulmai, su karfafa soyayya da yan uwantaka tsakaninsu, daga cikinsu akwai:

Yada sallama a tsakanin muslumai. Yada sallama na karfafa soyayya a tsakaninsu kamar yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya fada: "Ba zaku shiga aljanna ba har sai kun yi imani. Kuma ba zaku yi imani ba har sai kun so junanku. Shin baku so in nuna muku abinda in kuka yi shi zaku so junan ku? Ku yada sallama a tsakaninku". Buhari da Muslim ne suka rawaito shi. Kuma an tambayi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) shin wani (aikin) musulunci ne ya fi alheri? Sai yace: "Ka ciyar da abinci, kuma ka yi sallama ga wanda ka sani da kuma wanda baka sani ba". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Yin sallalolin farilla a masallaci tare da mutane; musulmai sukan hadu sau biyar a masallaci don yin sallar farillah, zasu yiwa junansu sallama, su yi musafaha da juna. Duk wadannan suna daga cikin abubuawan da suke karfafa soyayya da kauna, kuma su kawar da rarrabuwar kai.
Haka nan aikin hajji na hada kan musulmai daga duk kasashen duniya, inda suke haduwa wuri daya, kuma suna saka tufafi iri daya, kuma su yi dukkan ibadunsu tare babu banbanci.
Musayar kyaututtuka, saboda fadin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi): "Ku yi kyauta, zaku so junan ku". Lalle kyauta tana kara soyayya, kuma tana tafiyar da gaba da kiyayya.
Tausayawa bayin Allah. Allah Ya ce: "Saboda wata rahamar Allah ce daga gare shi ka zama mai sanyin hali a gare su. Kuma da ka kasance mai hushi, mai kaurin zuciya, da sun watse daga gare ka. Sai ka yafe musu laifinsu, kuma ka nema musu gafara, kuma ka yi shawara da su a cikin al'amarin". Suratu Al Imran: 159.
Haka kuma kyawawan dabi'u, da murmushi, da kaskantar da kai, da ziyartar juna, da cudanya da mutane cikin farin cikinsu da bakin cikinsu, da sauran kyawawan dabi'u da suke jawo soyayya a tsakanin mutane,

Allah madaukakin sarki Ya hada mu akan tafarkin gaskiya, Ya kuma cire duk wani gaba da kulli a tsakain mu,

Allah T ya kwato mana jagoranmu sayyid Ibrahim zakzaky {H} daga hannun azzalumai bijahee sayyadush shuhada'u.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post