MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATED
__________________________________________•
-Manzon Allah (S) yace, "Dabba tana da hakkoki shida (6) akan mai ita,
•
1- Duk lokacin dakai aiki da ita, dolene ka barta tai kiwo (taci abinci).
•
2- Dole kabata daman shan ruwa duk lokacin da kuka zo gifta wajen da ruwa yake.
•
3- Bazaka dake ta ba harsai ana bukatar hakan (ya cancanta, yazam dole).
•
4- Kada ka zuba mata kayan da yasha karfinta.
•
5- Karka saka ta tafiya mai nisan da bazata jure ba.
•
6- Kuma kada kake daukar dogon lokaci baka barta ta huta ba."
•
-A wani Hadisi kuma Manzon Allah (S) ya kara da cewa, " Kar ka doki dabba a fuska sabida lalle suna yabo ga Allah dayi masa tasbihi."
•
-Manzon Allah ya kara da cewa, " Ba wata dabba, koda kare ne da za'a kasheshi ba tare da hakki ba, face saiya kai karar mai kisan ranar alkiyama"
•
ΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦΦ
-Mustadrak Al-wasael Bugu Na 8, Shafi Na 258.
-Al-kafi Bugu na 6, Shafi 538.
-Kanz Al-Ummal Shafi 39968
•
__Bin Haroun Sigau√__