Ba Mallam Yakubu Yahaya, suke da nufin bakantawa ba, a'a suna kokarin bakanta Harkar Musulunci ne, Jagoranta da mabiya harkar baki daya a fadin kasar nan. Sanin kowa ne hatta makiyan mu sun mana shaida akan cewa bamu zagawa mu karbi taro da sisi wajan hukumomi domin tafiyar da wani abu a harkar.
Kaga dama wannan mukamin yana daga manyan abubuwan da suka rabamu da sauran mutane, kungiyoyi, 'Dariku, da sauran su, idan muka fara shikenan sai ace Laaaa! duk sun zama 1, hakan zai kashe dukkan ruhin gwagwarmayar na kokarin dawo da addini. Muda ko diyyan jinane aka mana tayi ba karba muke ba, ina ga tukuicin 5 da 10!
Su Mallam (H) sun faro tarbiyan wannann harkar ne da tsananin dogaro da kai, domin ni daga cikin manyan abubuwan da na koya daga Mallam Zakzaky akwai dogaro da kai, da kuma neman na kai. Shiyasa ma hatta wanda suke kallon mu daga nesa sun san haka kuma suna yawan fada a gaba da bayan idanun mu. Abinda nake fada Gwamnan Katsina ya bayyana haka kwanakin baya.
Ana bamu tarihi a kace lokacin da Abaca ya kama su Mallam a lokacin an shiga wani matsi na tattalin arziki a harkar yazama hatta kudin da za'a daukin nauyin buga Tuta da Banoni na yin Muzaharori ma yana wahala, sai akace wasu 'yanuwa sukayi nazarin a shirya wata babban Muzahara a Kaduna gameda halin da ake ciki aka tsara komai.
Amma babu kudin yin aikin, sai aka kawo shawarin ya wakilta 'yan uwa suje Ofishin Jakadancin Iran su nemi tallafin yin wannan aikin. masu ziyarar su Mallam din sunje da shawarin 'yan uwa gasu Mallam din, akace su Mallam suka rubuto a rubuce sukace “any body that control you financially will control you idiologically”
Abinda su Mallam suka rubuto a amsar shawarin nan sukace “duk wanda yayi iko dakai wajan tattalin arzikin ka, to zaiyi iko da kai a fikirar ka" wanda ke bamu labarin yace shi da idon shi yaga wannan takardan da rubutun su Mallam. Duba hatta Iran da muke koyi da salon Imam Kumaini nasu amma Mallam ya hana a tambaye su Naira, da wannan kawai ya isa tarbiyar dogoro da kai garemu duka.
Wani da yabani labari yace a gaban shi akayi, lokacin da Gwamna Masari yaci zabe, yana zagawa gaisuwa wajan manyan Malaman Addini wanda basu je sun tayashi murna ba, yazo wajan Mallam Yakub, yayi gaisuwa da ze tafi sai ya ajje makudan kudi, take Mallam din yace menene wannan? Nagode sosai amma bana bukata, Nagode, haka nan akayi kaman yanda ya fadamin.
Babu mamaki idan hakan yafaru, saboda Mallam Yakubu Dalibin Mallam Zakzaky abin mamakin shi ne ace Mallam Yakubu na karban na goro da na babban riga, sai muji mamaki muce, yaya akayi Mallam Zakzaky be samu nasarar tarbiyantan da wani tsayayyen mutum ko 1 ba?
—Bilya Dass
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Muhimman zantuka