Ana Cigaba Da Kashe-kashe A Katsina: Malamai Ya Kamata Su Fito Su Karbi Shugabancin Jama'a, Tunda Ƴan Siyasa Sun Kasa – Inji Farfesa Umar Labdo



Rahotanni na nuna ana ci gaba da kashe-karshen mutane a jihar Katsina da ma sauran jihohin Arewa maso Yammacin kasar nan duk da kokarin Gwamnati na tsayar da irin wadan nan kashe-kashe.

Ko a jiya da safe, kimanin karfe 10.00, yan ta'adda da aka kissima yawansu da 200 sun kai hari kauyen Yar Gamji na karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Sun iske manoma a gonakinsu, suka kashe mutane 15 a cikin harin da ya dauki tsawon awa guda. (Duba jaridar Daily Trust ta you, Talata 7/7/2020, Shafi na 4.)

Garin Yar Gamji kauye ne mai nisan kilomita 30 kacal daga garin Katsina, babban birnin jihar, a kan titin Dutsin Ma zuwa Kankara. Kada a mance a garin Katsina ne hedukwatar mayakan sama take wadanda aka tanade su don yaki da ta'addanci a jihohin Arewa maso Yamma.

Duk da kusancin kauyen Yar Gamji da garin Katsina, yan ta'addar sun ci karensu ba babbaka, kuma suka tafi abinsu, ba tare da kalubale ba daga jami'an tsaro, yan sanda ko soja, na sama ko na kasa.

Wannan abu yana da daure kai ainun. Mayaka dari biyu, su kwashe awa guda suna kisa dab da gari, amma babu wanda ya daga musu kara. A mota, minti 30 zai kai yan sanda garin daga Katsina, sojojin sama kuwa kafin jirginsu ya gama daidaita a sama sun isa garin. Don me ya sa babu wanda ya motsa?

Idan suka ce ba su da masaniya, wannan yana nuna cewa jami'an tsaronmu suna barci a bakin aiki! Idan sojojin da aka girke a babban birnin jiha don aikin ko-ta-kwana ba su da masaniya har abokan gaba su matso tafiyar kilomita 30, babu shakka akwai babbar matsala a cikin yanayin aikin dakarunmu. Ke nan sai an shigo garin sa'an nan za su farga? Fargar jaji?

Ina bangaren leken asiri na Sojin Nijeriya? Ina jami'an DSS gwanayen kwantan bauna da kame-kamen siyasa a Abuja? Kashe-kashen mutanenmu da ake yi a garuruwa da birane ba ji ba gani kuma ba kakkautawa, anya ba laujen yan siyasa a cikin nadin Gwamnati?

Ta yaya mayaka 200 za su zo gab da gari, su yi barna, kuma su bace bat kamar masu layar zana? Wane bayani mahukunta da shugabanni suke da shi dangane da wannan? Ko kuwa suna zaton ba ma bin su bashin bayani? Shin yaushe wannan kashe-kashen zai kare? Yanzu lokaci bai yi ba da shugabannin da suka gaza kare rayukan mutanensu da dukiyoyinsu da mutuncinsu za su aje aiki su koma gefe su yafa mayafin kunya? Ko kuwa sai an kai mutane bango?

Idan hukuma ta kasa, ta gajiya, to su mutane cewa aka yi su zauna su jira a zo a kashe su suna zaune, a kwashe dukiyoyinsu, a keta alfarmar iyalinsu? Idan Dimokradiyya ta kasa, gwamnati ta gaza, shugabanninmu sun basar da mu, shin a cikin addininmu da al'adunmu da tarihinmu mai tsawo da abin alfahari babu amsa ga wannan kalubalen?

Ina malamanmu? Idan mala'u sun kasa, ku ma ba ku da katabus? Me Manzon Allah (SAW) ya umarci Musulmi da su yi idan aka nemi rayukansu ko dukiyarsu ko mutuncinsu? Shin babu hadisi a kan wannan ko kuwa kun mance shi ne?

Ina kalubalantar malamai da su fito su karbi shugabancin jama'a, saboda mala'u sun kasa. Kafin malamai su kimtsa su fito, ina kira ga talakwa da a ci gaba da zangazanga. Ya kamata zangazanga ta barke a dukkan biranen Arewa kuma kada ta tsaya sai an dena kisa.

Babu uzuri ga wanda bai motsa be, matukar yana da sukunin motsawa.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post